An kori mutane 5 daga kasar Belgika yayinda suke kokarin kona Al-Kur'ani

An kori mutane 5 daga kasar Belgika yayinda suke kokarin kona Al-Kur'ani

- Ma'aikatar harkokin wajen Beljika ta fitittiki mutane biyar masu kokarin kona Al-Kur'ani

- Wadannan mutane sun shahara da tayar da zaune a tsaye ta hanyar shirya bikin kona littafi mai tsarki

Wasu yan kasar Denmark da ake zargin suna kokarin fusata Musulman kasar Belgika ta hanyar kona Al-Kur'ani sun shiga hannu kuma an fitar da su daga kasar.

A labarin da aka daura a shafin kungiyar ta Facebook, wadanda aka kama mambobin kungiyar “Stram Kurs” ne - wata kungiyar yan kasar Denmark masu yaki da Musulunci da kuma yan gudun Hijra karkashin jagorancin Rasmus Paludan.

A cewar shafin, an damke Paludan da kansa a kasar Faransa kuma an fitittikeshi.

Kungiyar Stram Kurs ta shahara wajen yin abubuwan tayar da zaune tsaye kuma hukumomin kasar Belgika sun samu labarin sun shirya bikin kona Al-Kur'ani a Molenbeek, wani gari da ke da adadin yan kasar Maroko da yawa.

Wata majiya ta bayyanawa AFP cewa an sanarwa yan sanda shirye-shiryen da suke yi.

KU KARANTA: Sarkin Saudiyya ya kira Buhari ta waya sun tattauna

An kori mutane 5 daga kasar Belgium yayinda suke kokarin kona Al-Kur'ani
An kori mutane 5 daga kasar Belgium yayinda suke kokarin kona Al-Kur'ani
Asali: UGC

KU DUBA: Bayan shekara dubu uku, an gano wata siffa a sansanin da sojojin Annabin Dauda suka mamaye a Golan

Sakataren harkokin wajen Belgium kan yan gudun Hijra, Sammy Mahdi, ya yi na'am da damke wadannan mutane biyar.

"An umurcesu su fita daga kasar ba tare da bata lokaci ba, kuma sun yi hakan," ofishinsa yace.

"An hana su zama saboda kasancewarsu a kasar Belgium matsala ne ga al'umma. An damke wani mutum a Faransa ta wannan dalili."

"Har da kasar jamus ta dauki irin wannan mataki kan wannan mutum (shugabansu), saboda jami'an tsaro sun dauke shi mai yada da'awar kiyayya."

A Agusta, rikici ya barke Malmo, kudancin kasar Sweden, inda wasu yan ta'adda suka kona Al-Kur'ani.

Mazauna garin suka yi zanga-zanga, suka kaiwa yan sanda hari.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel