Wanda ya hada bidiyon auren Buhari da Sadiya ya gurfana a gaban kotu
- Idan ba a manta ba, a watan Janairun 2020 ne bidiyon auren shugaban kasa Buhari da minista Sadiya Umar Faruk yayi ta yawo
- Hukumar DSS ta samu nasarar damke wani Kabiru Mohammed, wanda ake zargin shi ya kirkira bidiyon bikin
- Duk da DSS ta bukaci kada kotu ta bayar da belinsa, sai da ta bayar, bayan lauyansa ya gabatar da hujjoji ga kotu
An damki wanda ya hada bidiyon bogi na auren minista Sadiya Umar Faruk da shugaban kasa Muhammadu Buhari a watan Janairu.
An gurfanar dashi a gaban kotu bisa zargin hada bidiyon bogi.
Bayan zurfafa bincike, Hukumar DSS ta samu nasarar damko Kabiru Mohammed tun watan Janairu, amma bata gurfanar dashi gaban kotu ba sai ranar Talata.
Ta ce tana zarginsa da hada bidiyon na bogi, wanda hakan ya janyo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani.
Hada bidiyon bogin, ya janyo matsaloli ga iyalan ministan da shugaban kasa.
Hukumar DSS ta bukaci kotu da kada ta bayar da belinsa har sai an kammala duk binciken da za a yi a kansa, kuma ta nemi shawarar ma'aikatar shari'ar jihar Kano.
Sai dai kuma, Kotun ta bayar da belinsa, bayan lauya mai karesa ya gabatar da gamsassun hujjoji a kan cewa sam bai aikata laifin da ake zarginsa da shi ba.
An dage sauraron shari'ar har sai ranar 5 ga watan Fabrairun 2021.
KU KARANTA: Da duminsa: Jigo a fadar Buhari ya rasu sakamakon ciwon kansa
KU KARANTA: Yaki da Boko Haram ya dauka dogon lokaci - Gwamnan PDP
A wani labari na daban, wata tsohuwa mai shekaru 80, ta auri masoyinta mai shekaru 35 da haihuwa a kasar Egypt.
An daura auren Iris Jones da Mohammed Ahmed yanzu haka, bayan sun sha soyayyarsu ta shekara daya da 'yan watanni a kasar Egypt.
Matar mai shekaru 80 da haihuwa, ta hadu da mijin nata wuraren watan Yulin 2019 a wata matattara da ke kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, kuma sun yanke shawarar yin aure a cikin shekarar.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng