Gwarazan yan kwallon Najeriya sun dira Najeriya don karawa da Sierra Leone (Ga jerinsu)
Yayinda ake saura kwanaki uku wasan kwallon fidda gwanin gasar kofin nahiyar Afrika wanda akafi sani da AFCON tsakanin Najeriya da Sierra Leone, gwarazan yan wasan Super Eagles sun dira jihar Edo.
Yan kwallon a yau sun motsa jiki a filin kwallon San Ogbemudia dake birnin Benin tare da mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu.
Daga cikin yan wasan da suka hallara a cewar NFF sune:
Ahmed Musa
William Troost-Ekong
Alex Iwobi
Ola Aina
Joe Aribo
Leon Balogun
Kevin Akpoguma
Sebastin Osigwe
Zaidu Sanusi
Tyronne Ebuehi
Etebo Oghenekaro
Maduka Okoye
Ikechukwu Ezenwa
Chidozie Awaziem
Kelechi Iheanacho
Emmanuel Dennis

Asali: Twitter
KU DUBA: Ahmed Musa, dan wasan Super Eagles, ya wallafa bidiyon sabuwar motarsa kirar Benz Vito
Mun kawo muku a baya cewa an saki ranakun buga wasar fidda gwanin gasar kasashen nahiyar Afrika tsakanin Najeriya da kasar Sierra Leone.
Wanna itace wasa ta farko da yan kwallon Najeriya zasu buga domin samun gurbin shiga sahun kasashen da zasu kara a gasar Afcon 2022.
Za'a buga wasanni biyu tsakanin dukkan kasashe; daya a gida, daya a waje.
A wasar farko, Najeriya zata karbi bakuncin yan kwallon kasar Sierra Leone a filin kwallon Samuel Ogbemudia dake birnin Benin, jihar Edo.
Za'a buga wasar ranar Juma'a, 13 ga watan Nuwamba, 2020.
Bayan haka yan kwallon Najeriya zasu garzaya filin kwallon Siaka Stevens dake Freetown, kasar Sierra Leone ranar 17 ga Nuwamba, 2020.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng