An saki ranakun buga wasar fiddan gwanin gasar AFCON tsakanin Najeriya da Sierra Leone

An saki ranakun buga wasar fiddan gwanin gasar AFCON tsakanin Najeriya da Sierra Leone

- Kungiyar kwallon kafar nahiyar Afrika ta fara shirye-shiryen gasar kwallon kasashen nahiyar da za'a yi a shekarar 2022

- Za'a fara wasanni fidda gwani tsakanin dukkan kasashen nahiyar

- Wadanda suka samu nasara zasu kara a gasar ta AFCON

An saki ranakun buga wasar fiddan gwanin gasar kasashen nahiyar Afrika tsakanin Najeriya da kasar Sierra Leone.

Wanna itace wasa ta farko da yan kwallon Najeriya zasu buga domin samun gurbin shiga sahun kasashen da zasu kara a gasar Afcon 2022.

Za'a buga wasanni biyu tsakanin dukkan kasashe; daya a gida, daya a waje.

A wasar farko, Najeriya zata karbi bakuncin yan kwallon kasar Sierra Leone a filin kwallon Samuel Ogbemudia dake birnin Benin, jihar Edo.

Za'a buga wasar ranar Juma'a, 13 ga watan Nuwamba, 2020.

Bayan haka yan kwallon Najeriya zasu garzaya filin kwallon Siaka Stevens dake Freetown, kasar Sierra Leone ranar 17 ga Nuwamba, 2020.

KU KARANTA: Kuma dai: Yan bindiga sun kai mummunan hari jihar Zamfara, sun halaka mutum 4

An saki ranakun buga wasar fiddan gwanin gasar AFCON tsakanin Najeriya da Sierra Leone
An saki ranakun buga wasar fiddan gwanin gasar AFCON tsakanin Najeriya da Sierra Leone Credit: @thenff
Asali: Twitter

Hakazalika, Kungiyar kwallon Najeriya NFF ta saki jerin sunayen yan kwallon Najeriyan da aka gayyata domin buga wadannan wasanni.

Daga cikinsu akwai masu tsaron gida Daniel Akpeyi, Maduka Okoye da Osigwe.

Masu tsaron bayan kuwa akwai Chris Ekong, Kenneth Omeruo, John Balogun, Chinedu Awaziem, Zaidu Sanusi, Ola Aina, Jamilu Collins, Femi Ajayi da Akpoguma.

Yan tsakiya kuwa akwai, Oghenekaro Etebo, Joseph Aribo, Ebuehi da Onyeka.

Yan gaba kuwa akwai Ahmed Musa, Moses Simon, Victor Osimhen, Kelechi Iheancho, Samuel Chukwueze, Ejuke, Dennis Bonaventure, da Alex Iwobi.

DUBA NAN: Gwamna Abdullahi Ganduje ne jagoran yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya - Dawisu

An saki ranakun buga wasar fiddan gwanin gasar AFCON tsakanin Najeriya da Sierra Leone
An saki ranakun buga wasar fiddan gwanin gasar AFCON tsakanin Najeriya da Sierra Leone Hoto: @thenff
Asali: Twitter

A bangare guda, shahrarren dan wasan kasar Juventus Cristiano Ronaldo ta samu waraka daga muguwar cutar nan mai toshe numfashi watau Coronavirus, kungiyar ta tabbatar ranar Juma'a.

"Ronaldo ya yi gwajin cutar. Sakamakon ya nuna cewa ya samu waraka," Juventus tace.

"Saboda haka, dan kwallo ya warke bayan kwanaki 19 kuma babu bukatar killace kansa yanzu."

Ronaldo ya kamu da cutar COVID-19 ne ranar 13 ga watan Oktoba yayin wasar kasarsa, Portugal. Ya killace kansa tun lokacin da ya kowa Italiya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel