Yaki da Boko Haram ya dauka dogon lokaci - Gwamnan PDP

Yaki da Boko Haram ya dauka dogon lokaci - Gwamnan PDP

- Kawo karshen Boko Haram yana daukar lokaci mai tsawo, cewar Gwamna Bala Mohammed

- Gwamnan jihar Bauchi, ya ce babban abin kunya ne ace har yanzu ba a fatattaki 'yan Boko Haram ba

- Ya fadi hakan ne lokacin da kwamitin 'yan majalisar wakilai suka kai masa ziyara

Gwamna Bala Mohammed ya nuna takaicinsa a kan yadda yakar Boko Haram yake daukar lokaci mai tsawo.

Gwamnan jihar Bauchin yayin da kwamitin 'yan majalisar wakilai a kan sojoji suka kai masa ziyara a gidan gwamnati a ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamba, ya ce wannan babban abin kunya ne a ce har yanzu ba a kawo karshensu ba.

KU KARANTA: Da duminsa: Munirat Abdulsalam ta bar Musulunci, ta bayyana dalilinta

A cewar Bala; "Duk da mutum mai kwazo irin Femi Gbajabiamila ne ke jagorantar majalisar wakilan.

"Shiyasa mafi yawan 'yan kwamitin ba daga arewa maso gabas suke ba.

"Ku taimaka, ku samar mana da kwanciyar hankali. Idan ba a kawo karshen wannan al'amarin ba, zai zama abin kunya. An dade ana yin abu daya."

Sannan ya yi tsokaci a kan tsanantuwar 'yan ta'adda da masu satar shanu wanda ya janyo sojoji suna ayyukan 'yan sanda, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

"Sojoji kullum bukatar makamai da kayan aiki suke yi, sun gaji, saboda ba za ka hada yawansu da na 'yan Najeriya ba."

Yaki da Boko Haram ya dauka dogon lokaci - Gwamnan PDP
Yaki da Boko Haram ya dauka dogon lokaci - Gwamnan PDP. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bayan shan mugun kaye, matar Trump ta shirya tsinke igiyar aurensu - Tsohuwar hadimarta

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, ya ce ba zai bar tattaunawa da 'yan ta'addan jiharsa ba. Yace tattaunawar tana da matukar muhimmanci don neman zaman lafiya a jihar, Vanguard ta ruwaito.

Gwamnan ya sanar da hakan a wata takarda da Zailani Bappa, mai bashi shawara na musamman a harkar labarai, inda yace sun samu nasarar ceto mutane 26 daga jihar Katsina masu shekaru 8 zuwa 12 daga hannun 'yan ta'adda ba tare da biyan ko sisi ba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel