Ba zan daina tattaunawa da 'yan bindiga domin neman sasanci ba - Gwamnan Zamfara

Ba zan daina tattaunawa da 'yan bindiga domin neman sasanci ba - Gwamnan Zamfara

- Gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, ya ce ba zai daina tattaunawa da 'yan ta'adda ba don ta haka ne kadai za a samu zaman lafiya

- Ya fadi hakan ne bayan an samu nasarar ceto yara 26 'yan asalin jihar Katsina, wadanda masu garkuwa da mutane suka kai su jihar Zamfara

- Gwamnan ya tabbatar da an duba lafiyar yaran, an basu sutturu sannan an mayar da su gidajensu, ta hannun kwamishinan jihar, Abubakar Dauran

Gwamnan jihar Zamfara, Muhammad Bello Matawalle, ya ce ba zai bar tattaunawa da 'yan ta'addan jiharsa ba.

Yace tattaunawar tana da matukar muhimmanci don neman zaman lafiya a jihar, Vanguard ta ruwaito.

Gwamnan ya sanar da hakan a wata takarda da Zailani Bappa, mai bashi shawara na musamman a harkar labarai, inda yace sun samu nasarar ceto mutane 26 daga jihar Katsina masu shekaru 8 zuwa 12 daga hannun 'yan ta'adda ba tare da biyan ko sisi ba.

Kamar yadda takardar ta bayyana, yara matan da aka yi garkuwa da su, 'yan karamar hukumar Faskari ne da ke jihar Katsina, wadanda 'yan bindigan suka kai su Zamfara.

A cewarsu, gwamnatin jihar ta gano inda suke kuma Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Alhaji Abubakar Dauran ya tattauna dasu kafin su saki yaran.

"Lokaci bayan lokaci, Dauran yana kokarin tattaunawa da su a maimakon gwamnan don kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar," a cewarsu.

Yayin da aka amshi yaran , Gwamna Matawalle ya ce mulkinsa ba zai zura ido ya bar tattauanawa da su ba, saboda harbi da yakin 'yan ta'adda ba zai magance matsalar ba.

Ya ce ba za su sadaukar da rayukan yara ba don kawai su faranta wa wasu rai ba.

An tabbatar da lafiyar yaran guda 26 'yan jihar Katsina, masu shekaru 8 zuwa 12 da haihuwa da aka samu nasarar cetowa, an basu sutturu sannan an mayar da su gidajensu.

KU KARANTA: Sojoji sun tarairaya masu zanga-zanga, har ruwa da lemu suka raba a Lekki tollgate - Kwamanda

Ba zan daina tattaunawa da 'yan bindiga domin neman sasanci ba - Gwamnan Zamfara
Ba zan daina tattaunawa da 'yan bindiga domin neman sasanci ba - Gwamnan Zamfara. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: UGC

KU KARANTA: Batanci ga Annabi: An kafa sharudda 4 a kan mika Rahama Sadau gaban kotu

A wani labari na daban, dakarun sojin saman Najeriya sun yi wa 'yan bindiga ruwan wuta ta jirgin yaki a yankin Kuzo da ke jihar Kaduna.

Rundunar karkashin Operation Thunder Strike ta tabbatar da kisan 'yan bindiga masu yawa a wannan samamen da ta kai.

Kamar yadda bidiyon da hedkwatar tsaro ta wallafa a shafinta na Twitter ya bayyana, sojin saman ta jiragen yaki sun tare 'yan bindigar a Kuzo yayin da suke kokarin fitar da shanun sata daga dajin.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng