Da duminsa: Munirat Abdulsalam ta bar Musulunci, ta bayyana dalilinta

Da duminsa: Munirat Abdulsalam ta bar Musulunci, ta bayyana dalilinta

- Fitacciyar malamar mata mai magana a kan auratayya a kafafen sada zumuntar zamani, ta bar addinin Musulunci

- Ta sanar da hakan a wata wallafar da tayi a shafinta na kafar sada zumuntar zamani ta Facebook a ranar Lahadi

- Kamar yadda tace, bata so a sake alakanta ta da addinin Islama duk da shekaru biyu da tayi a cikinsa

Munirat Abdulsalam, fitacciyar malamar mata kuma mai tattaunawa a kan harkar auratayya, ta bar addinin Musulunci.

Idan za mu tuna, kusan shekaru biyu da suka gabata ne ta dawo addinin Islama inda aka lakana mata kalmar shahada tare da nuna mata wankan komawa addinin Musulunci a babban masallacin kasa da ke Abuja.

Kwatsam, a jiya Lahadi sai ga wata wallafarta a shafinta na Facebook wacce ta janyo cece-kuce.

Kamar yadda ta wallafa, "Daga yau, bana so a sake danganta ni da Musulunci, domin a cikin shekaru biyu da suka gabata bayan na karba addinin, ban tsinci komai ba da ya wuce barazanar kashe ni, zagi da kirana sunaye.

"Ba su taba daukata a matsayin daya daga cikinsu ba balle su nuna min wata kauna a matsayina na marainiya kuma yarinya mace da ta tashi a wannan al'ummar.

"Abu daya nake bukata shine a karrama ni kuma a karbeni, wanda na gaji har yanzu ban samu ba. Za ku iya kasheni a yanzu idan kun ga dama, amma na gaji da wannan tsangwamar."

KU KARANTA: Ba zan daina tattaunawa da 'yan bindiga domin neman sasanci ba - Gwamnan Zamfara

Da duminsa: Munirat Abdulsalam ta bar Musulunci, ta bayyana dalilinta
Da duminsa: Munirat Abdulsalam ta bar Musulunci, ta bayyana dalilinta. Hoto daga en.videos2be.com
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Bidiyon soji suna ragargazar 'yan bindiga suna tsaka da taronsu a Kaduna

A wani labari na daban, daya daga cikin manyan 'yan fashin Najeriya, Shina Rambo, ya bayyana a babban birnin Ekiti, yana cewa shifa ya canja, yanzu haka ya koma kira ga addinin Kirista.

Ya yi wannan maganar ranar Lahadi a wani shiri na karshen mako da gidan rediyon Fresh FM, da ke Ado Ekiti, kuma dama shirin babban mawakin yabo ne, sannan mai gidan rediyon da kansa, Yinka Ayefele.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng