Bayan shan mugun kaye, matar Trump ta shirya tsinke igiyar aurensu - Tsohuwar hadimarta

Bayan shan mugun kaye, matar Trump ta shirya tsinke igiyar aurensu - Tsohuwar hadimarta

- Yanzu haka, matar Donald Trump, Melania, tana jiran ranar da za su bar White House ne, ta dankara masa saki, cewar tsohuwar hadimar matar Trump

- Hadimar mai suna Stephanie Wolkoff, ta bayyana hakan ne inda tace da Melania za ta yi yunkurin barin White House yana kan mulki, da ya azabtar da ita

- Akwai wata majiya daga wata hadimar daban, wacce tace yanzu haka auren Trump da Melania ya kare, lokacin saukarsa mulki kawai take jira ta rabu da shi

Melania, matar Trump tana neman sakinsa, mintina kadan da shan kayensa, cewar tsohuwar hadimar Trump, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Kamar yadda rahotonni suka bayyana, tsohuwar hadimar Trump ta ce Melania na neman sakin mijinta bayan ya fita daga White house.

Kamar yadda tsohuwar hadimar Trump din tace, matarsa na jiran lokacin da za su kwashe ya-nasu ya-nasu su bar gidan gwamnati, ita kuma za ta sake shi.

Har yanzu Trump bai amince da kayen da Joe Biden yayi masa ba, duk da ya zarcesa da kuri'un zaben kwaleji 270.

KU KARANTA: Bidiyon soji suna ragargazar 'yan bindiga suna tsaka da taronsu a Kaduna

Bayan shan mugun kaye, matar Trump ta shirya tsinke igiyar aurensu - Tsohuwar hadimarta
Bayan shan mugun kaye, matar Trump ta shirya tsinke igiyar aurensu - Tsohuwar hadimarta. Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hotunan giya ta N200m da hukumar Hisbah ta ragargaza a Kano

Tsohuwar hadimar Melania, Stephanie Wolkoff, wacce kwannan ta saki wani littafi, ta bayyana wa duniya cewa yanzu haka Melania ta fara kulla wata yarjejeniya, wacce tace za ta ba wa danta Barron nasa kason cikin dukiyar Trump.

A wani rahoto da The Mail Online suka saki, sun yi ikirarin tsohon hadiminta, Omarosa Manigault Newman ya ce, auren Melania da Trump mai shekaru 15 yanzu haka ya mutu.

A cewarsa: "Yanzu haka Melania na jiran lokacin da Trump zai sauka daga karagar mulkin Amurka, yadda za su rabu.

"Da Melania za ta yi yunkurin wulakanta shi ta rabu da shi yana karagar mulki, to da yayi amfani da wata hanyar da zai ladabtar da ita."

Akwai wani rahoto wanda ya bayyana yadda Melania ba ta yi tunanin mijinta zai ci zaben 2016 ba, bayan ta ji labarin ya ci, ta fashe da kuka.

A wani labari na daban, daya daga cikin manyan 'yan fashin Najeriya, Shina Rambo, ya bayyana a babban birnin Ekiti, yana cewa shifa ya canja, yanzu haka ya koma kira ga addinin Kirista.

Ya yi wannan maganar ranar Lahadi a wani shiri na karshen mako da gidan rediyon Fresh FM, da ke Ado Ekiti, kuma dama shirin babban mawakin yabo ne, sannan mai gidan rediyon da kansa, Yinka Ayefele.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel