Nagartattun halaye 9 na Bamalli da na duba na nada shi Sarkin Zazzau - El-Rufai

Nagartattun halaye 9 na Bamalli da na duba na nada shi Sarkin Zazzau - El-Rufai

- A ranar Litinin aka yi bikin nadin sarautar Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, inda aka bashi sandar mulki kuma aka gabatar masa da ma'aikatan fada

- Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi jawabi mai daukar hankali, inda ya fadi halayen 9 masu birgewa wadanda suka janyo ya zabi sabon sarkin

- A cewarsa, sarkin yana da halaye 9, wadanda suka hada da fasaha, ilimi, tausayi, kirki, kyakkyawar mu'amala, sanin yakamata, hakuri da juriya

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya bayyana halaye 9 wadanda suka dace da na sarakunan addini da suka janyo ya nada Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, a matsayin sarkin Zazzau.

Yayin da gwamnan yayi jawabi wurin kaddamar da nadin sabon sarkin da kuma gabatarwa da sarkin ma'aikatan fadarsa da aka yi a ranar Litinin a Zaria, gwamnan ya ce halayen sabon sarkin masu ban sha'awa sun hada da fasaha, ilimi, tausayi, kirki, kyakkyawar mu'amala, sanin yakamata, hakuri da juriya.

Kamar yadda gwamnan yace, ba wadannan kadai ne halayen Bamalli na kirki ba, har da dagewa wurin yin aiki tukuru a duk wuraren da ya taba yin aiki, don haka ya zama abin alfaharin masarautar da jihar gabadaya.

Yayin da yake taya sabon sarkin murna a madadin jihar Kaduna da mutanen Zazzau, El-Rufai ya rokesa da yayi kokarin tattara duk wata gogewar da ya samu a wuraren da yayi aiki, na gwamnati da masu zaman kansu, wurin tafiyar da mulkin masarautar.

Gwamnan ya roki sarkin, da yayi kokarin dasawa daga inda sauran sarakuna suka tsaya, sannan ya tabbatar ya tattaro duk 'yan sauran gidajen sarautar an dama dasu, Daily Nigerian ta ruwaito.

Ya roki sarkin, da ya bi irin turbar kakan mallawa, Alu dan Sidi, wanda yayi mulki shekaru 100 da suka wuce kafin turawan mulkin mallaka su tubesa.

Ya kara da rokar mutanen Zazzau da na kasa da su taru su yi biyayya a garesa.

KU KARANTA: Babban mai mukami a Zamfara ya fadi ya mutu a wurin bikin diyar Sanata Yarima (Hotuna)

Nagarta 9 ta Bamalli da na duba na nada shi Sarkin Zazzau - El-Rufai
Nagarta 9 ta Bamalli da na duba na nada shi Sarkin Zazzau - El-Rufai. Hoto daga @GovKaduna
Asali: Twitter

KU KARANTA: Bayan shan mugun kaye, matar Trump ta shirya tsinke igiyar aurensu - Tsohuwar hadimarta

A wani labari na daban, bayan sanar da sabon Sarkin Zazzau da Gwamna Nasir El-Rufai yayi, a ranar 9 ga watan Nuwamba ne yake mika masa sandar sarautar kasar Zazzau.

Ku biyo Legit.ng inda za ta dinga kawo muku abinda ke faruwa a filin Alhaji Muhammadu Aminu kai tsaye.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel