Babban mai mukami a Zamfara ya fadi ya mutu a wurin bikin diyar Sanata Yarima (Hotuna)

Babban mai mukami a Zamfara ya fadi ya mutu a wurin bikin diyar Sanata Yarima (Hotuna)

- Allah ya yi wa Dakta Malami Aliyu Yandoto rasuwa a ranar Asabar, a taron bikin diyar Yarima

- Yandoto shine shugaban hukumar kananan hukumomi ta jihar Zamfara kuma ya rasu bayan yanke jiki da yayi ya fadi

- Yandoto ya taba yin kwamishinan aikin noma sannan ya yi shugaban INEC na jihar Zamfara kafin rasuwarsa

Shugaban hukumar kananan hukumomi ta jihar Zamfara, Dakta Malami Aliyu Yandoto mai shekaru 57 a duniya ya yanke jiki ya fadi, tare da mutuwa a wurin bikin diyar Sanata Ahmed Sani Yerima da dan Sanata Adamu Aliero.

An yi daurin auren a gidan Yarima da ke Sokoto a ranar Asabar, 7 ga watan Nuwamban 2020 kuma ya samu halartar manyan 'yan siyasa, jiga-jigai da kuma kusoshin gwamnati da suka hada da shugaban majalisar dattawan Najeriya.

An gano cewa, bayan daurin auren, bakin da suka samu halarta sun garzaya gidan gwamnatin jihar Sokoto domin liyafar cin abincin rana.

Bayan isar mamacin tare da gwamnan jihar Zamfara, Bello Matwalle da wasu baki gidan gwamnatin, ya yanke jiki ya fadi inda yace ga garinku.

Da gaggawa aka hanzarta kai shi asibiti a Sokoto inda aka tabbatar da mutuwarsa, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Yandoto ya taba shugabancin hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Zamfara inda daga bisani yayi kwamishinan aikin noma na jihar Zamfara.

Gwamna Bello Matawalle ya nada shi shugaban hukumar kananan hukumomi na jihar, mukamin da ya rasu a kai kenan.

An birnesa kamar yadda addinin Islama ya tanada a ranar Lahadi da safe a garin da ke karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

Babban mai mukami a Zamfara ya fadi ya mutu a wurin bikin diyar Sanata Yarima (Hotuna)
Babban mai mukami a Zamfara ya fadi ya mutu a wurin bikin diyar Sanata Yarima (Hotuna). Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Batanci ga Annabi: An kafa sharudda 4 a kan mika Rahama Sadau gaban kotu

Babban mai mukami a Zamfara ya fadi ya mutu a wurin bikin diyar Sanata Yarima (Hotuna)
Babban mai mukami a Zamfara ya fadi ya mutu a wurin bikin diyar Sanata Yarima (Hotuna). Hotodaga @Lindaikeji
Asali: Twitter

Babban mai mukami a Zamfara ya fadi ya mutu a wurin bikin diyar Sanata Yarima (Hotuna)
Babban mai mukami a Zamfara ya fadi ya mutu a wurin bikin diyar Sanata Yarima (Hotuna). Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sojoji sun tarairaya masu zanga-zanga, har ruwa da lemu suka raba a Lekki tollgate - Kwamanda

Babban mai mukami a Zamfara ya fadi ya mutu a wurin bikin diyar Sanata Yarima (Hotuna)
Babban mai mukami a Zamfara ya fadi ya mutu a wurin bikin diyar Sanata Yarima (Hotuna). Hoto daga @Lindaikeji
Asali: Twitter

A wani labari na daban, dakarun sojin saman Najeriya basu dauka kiran da aka dinga musu ba domin su kawo dauki ga jama'ar kauyen Takulashi da ke gundumar Shikarkir a karamar hukumar Chibok ta jihar Borno, majiyoyi daga rundunar ta tabbatar wa The Cable.

Wurin karfe 10 na safiyar Lahadi, wasu mayakan ta'addanci sun tsinkayi kauyen inda suka dinga harbe-harbe sannan suka banka wa gidaje wuta.

Majiyoyi daga mazauna kauyen sun sanar da cewa a kalla rayuka 11 suka salwanta kafin zuwan dakarun da ke Chibok.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel