Gangaran ka fi gwani: Rayuwa da mutuwar Sheikh Noreen Muhammad Siddiq

Gangaran ka fi gwani: Rayuwa da mutuwar Sheikh Noreen Muhammad Siddiq

- Allah ya yiwa Sheikh Noreen Muhd Sadiq Assudaniy rasuwa, sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da shi

- Sheikh Noreen ya kasance gangaran a fagen karatun Al-Qur'ani mai girma daga kasar Sudan

- Hafizin ya rasu ne tare da wasu yan uwansa hafizai su uku a hanyarsu ta dawowa daga da’awa a taron Maulidin Annabi Muhammad a yankin Shmaliya

A yammacin ranar Juma’a, 6 ga watan Nuwamba ne aka sami labarin rasuwar shahararren hafizin nan na Al-Kur’ani mai girma, Sheikh Noreen Muhammad Siddiq na kasar Sudan.

An kuma yi jana’izarsa a safiyar ranar Asabar, 7 ga watan Nuwamba a Khartoum.

Sheikh Noreen wanda ya kasance gagara-misali a fagen karatun Al-Qur'ani mai girma ya rasu ne sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da shi.

Gangaran ka fi gwani: Rayuwa da mutuwar Sheikh Noreen Muhammad Siddiq
Gangaran ka fi gwani: Rayuwa da mutuwar Sheikh Noreen Muhammad Siddiq Hoto: AlKhaleej Today
Asali: UGC

Marigayi Noreen ya amsa wata gayyata da aka masa ne zuwa yankin Shmaliya wato arewacin Sudan ne domin yin da'awah tare da wasu malamai hudu a garin Halfa.

Sun yi nasarar isa garin sannan kuma suka aiwatar da ayyukan da suka kai su.

Sai dai suka hadu da ajalinsu a hanya inda motarsu ta yi taho mugama ne da wata babbar mota a kusa da birnin Omdurman.

KU KARANTA KUMA: Kada ki bari ayi tonetone: Fati Slow ta yi kacakaca da Mansura Isa (bidiyo)

An haifi mariagyi Shehin malamin a shekaru 38 da ta gabata a wani gari mai suna Farajab a cikin kasar Sudan.

Marigayin ya yi makarantar allo a garin Khorsi a shekarar 1998, kuma shi dalibin wani babban malami ne mai suna Sheikh Makki a Sudan.

Daga nan sai ya ci gaba da neman ilimin addinin Musulunci duk a garin Khorsi, inda ya shafe tsawon shekaru 20 yana neman ilimi a karkashin malamai daban-daban.

A haka ne dai marigayin ya zama almajirin Sheikh Makki a Khartoum, babban birni kasar Sudan.

Bayan ya koma karkashin Sheikh Makki, ya koyi salon kira'arsa wadda ake kira ‘Kira'ar Daubit’.

KU KARANTA KUMA: Batanci ga Annabi: An kafa sharudda 4 a kan mika Rahama Sadau gaban kotu

Na kusa da marigayin, Sheikh Khidir ya ce Sheikh Noreen mutum ne mai saukin kai, inda yace koda karamin yaro ne ya nemi ya biya masa karatun Al-Kur'ani lallai zai tsaya ya yi masa, sashin Hausa na BBC ta ruwaito.

A cewarsa wannan dalili ne ya sa ya shahara kuma ya sami daukaka a gurin jama'a cikin dan kankanin lokaci.

Marigayi Sheikh Noreen ya mutu ya bar matan aure hudu da 'ya'ya takwas.

A wani labarin, Shaharren mutumin nan ma kama barayi da 'yan fashi a Najeriya Ali Kwara Azare ya rasu a ranar Juma'a 6 ga watan Nuwamban 2020.

Ali Kwara ya rasu ne a babban birnin tarayya Abuja bayan ya yi fama da jinya kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Marigayin ya rasu ya bar matar aure daya da yara hudu da 'yan uwa da dangi da dama. An haife Ali Kwara ne a garin Azare da ke ƙaramar hukumar Katagum a jihar Bauchi.

Ya shahara sosai wajen kama barayi da cikin dazuzzuka sannan daga bisani ya ladabtar da su ya kuma koya musu sana'a da su rike kansu da ita.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel