Ali Ƙwara Azare 'mai kama ɓarayi' ya riga mu gidan gaskiya

Ali Ƙwara Azare 'mai kama ɓarayi' ya riga mu gidan gaskiya

- Allah ya yi wa fitaccen mai kama 'yan fashi da barayi Ali Kwara rasuwa a ranar Juma'a

- Marigayin ya rasu ne a garin Abuja bayan fama da rashin lafiya

- Iyalansa sun sanar da cewa za a yi janaizarsa a mahaifarsa ta Azare da ke jihar Bauchi

Shaharren mutumin nan ma kama barayi da 'yan fashi a Najeriya Ali Kwara Azare ya rasu a ranar Juma'a 6 ga watan Nuwamban 2020

Ali Kwara ya rasu ne a babban birnin tarayya Abuja bayan ya yi fama da jinya kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Yanzu-yanzu: Ali Kwara 'mai kama barayi' ya riga mu gidan gaskiya
Yanzu-yanzu: Ali Kwara 'mai kama barayi' ya riga mu gidan gaskiya. Hoto: BBC Hausa/ Nazif Babaji
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Ba ku isa kuyi mana mulkin mallaka ba - Kungiyar Dattijan kudu ga gwamnonin Arewa

Marigayin ya rasu ya bar matar aure daya da yara hudu da 'yan uwa da dangi da dama.

An haife Ali Kwara ne a garin Azare da ke ƙaramar hukumar Katagum a jihar Bauchi.

Ya shahara sosai wajen kama barayi da cikin dazuzzuka sannan daga bisani ya ladabtar da su ya kuma koya musu sana'a da su rike kansu da ita.

KU KARANTA: Zaɓen Amurka: Magoya bayan Trump sunyi zanga-zanga a ofishin ƙidayar ƙuri'u ta Arizona

Danginsa sun bada sanarwar cewa za a gudanar da jana'izarsa a mahaifansa ta Azare.

A wani labarin, kun ji cewa Jami'an Hukumar Kiyayye Hadurra na Kasa, FRSC, za su fara amfani da bindiga don kare kansu daga sharrin wasu masu amfani da tituna a Najeriya.

Akinfolarin Mayowa, shugaban kwamitin FRSC a majalisar wakilai ta kasa ne ya sanar da hakan yayin kare kasafin kudin hukumar na 2021 a ranar Alhamis 5 ga watan Nuwamba a Abuja.

Akinfolarin Mayowa ya yi bayanin cewa dokar ta FRSC ACT na 1992 ta bawa jami'an hukumar ikon rike bindiga.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel