Karya ake mun, ban ce a hana Buhari zuwa asibitin ƙasar waje ba - Sanata La'ah
- Shugaban kwamatin raba daidi na majalisar dattawa, Sanata Danjuma La’ah, ya nisanta kansa daga rahoton cewa ya nemi a hana Buhari zuwa asibitin waje
- La'ah ya ce shi dai ya nemi a inganta asibitin fadar shugaban kasa ta yadda za ta iya kula da shugaban kasar da sauran manyan gwamnati
- Babban Sakataren fadarshugaban kasa, Tijani Umar, ya gabatar da kasafin biliyan N19.7 wanda daga ciki aka ware N1.3b don kulawa da inganta asibitin Fadar Shugaban Kasa
Shugaban kwamitin majalisar dattijai a kan tabbatar da daidaito da alaka a tsakanin bangarorin gwamnati, Sanata Danjuma La’ah, ya karyata rahoton da ke cewa ya bukaci a hana Shugaban kasa Muhammadu Buhari tafiya kasashen wajen neman magani.
A cewar Sanata La’ah, shi dai ya nemi a inganta asibitin fadar Shugaban kasa da duk abun da ya kamata ta yadda zai iya bayar da cikakken kula ga Shugaban kasar da manyan jami’an gwamnati, ta yadda ba sai sun je kasar waje ba.
“Babu wanda na nemi ya dakatar da Buhari daga tafiya duba lafiyarsa a kasashen waje”, La’ah ya bayyana wa ’yan jarida kamar yadda Aminiya ta ruwaito.
KU KARANTA KUMA: Bayan nadamar ta: Rahama Sadau ta bayyana halin da take ciki na rashin kwanciyar hankali

Asali: UGC
KU KARANTA KUMA: Bayan nadamar ta: Rahama Sadau ta bayyana halin da take ciki na rashin kwanciyar hankali
A baya mun ji cewa majalisar dattijai ta gargadi ma'aikatan fadar shugaban kasa (Asorock Villa) su dakatar da shugaba Buhari daga fita waje domin a duba lafiyarsa.
Kwamitin majalisar dattijai a kan tabbatar da daidaito ne ya yi wannan gargadi yayin da babban sakataren fadar shugaban kasa, Tijjani Umar, ya bayyana a gabansa domin kare kasafi kudin shekarar 2021.
Umar, ya gabatar da kasafin biliyan N19.7 wanda daga ciki aka ware Naira biliyan 1.3 don kulawa da inganta asibitin Fadar Shugaban Kasa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng