Na kusa zubar da hawaye saboda ganin irin barnar da akayi a Legas - Gwamna El-Rufai

Na kusa zubar da hawaye saboda ganin irin barnar da akayi a Legas - Gwamna El-Rufai

- Duk mai son ci gaba dole ya zubar da hawaye idan yaga irin barnar da aka yi wa Legas

- El-Rufai ya bayyana cewa matasan da suka lalata dukiyoyi a Legas kansu suka cuta

- Gwamnatin Kaduna ta jajantawa Rundunar 'yan sanda da sauran wanda rikicin ya shafa a Legas

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, yakai ziyara jihar Legas a ranar Alhamis inda ya hadu da takwaransa na jihar, Babajide Sanwa-Olu, don jajanta masa akan mace-mace da kuma dukiyoyin da aka rasa a jahar baya-bayan nan.

Sakamakon bata garin da suka kawo wa zanga zangar #EndSARS cikas ta hanyar yin mummunar barna a Lagos watan da ya gabata.

El-Rufai ya ce Sanwa-Olu yayi iyakacin abin da zai iya don ganin ba a tada hargitsi ba, amma wanda zuciyar su ba komai sai tada hankali, suka yi amfani da zanga zangar wajen cimma bukatun su.

Na kusa zubar da hawaye saboda ganin irin barnar da akayi a Legas - Gwamna El-Rufai
Na kusa zubar da hawaye saboda ganin irin barnar da akayi a Legas - Gwamna El-Rufai. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Alkali ya bada belin Naziru Sarkin Waƙa

A wata sanarwa da Sakataren yada Labaran gwamna Sanwa-Olu, Gboyega Akosile ya fitar, gwamnan Kaduna ya kusa zubar da hawaye da yaga hotunan irin barnar da aka yi wa jahar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Sanarwar mai taken, 'El-Rufai: matasan da suka lalata dukiyoyin gwamnati a Lagos kan Su suka cuta.'

An jiyo El-Rufai yana cewa, "Na dauki tsawon lokaci don duba Hotunan irin barnar da akayi wasu dukiyoyi a Lagos kuma sai da na kusa zubar da hawaye. Duk me son ci gaba dole ne ya zubar da hawaye idan ya ga irin barnar da akayi wa dukiyoyin gwamnati da kuma wuraren da suka samarwa matasa ayyukan yi.

"Nuna kyamar zaluncin yan sanda dai dai ne, amma lalata kadarorin gwamnati, wanda dole sai an kashe makudan kudaden da ya kamata a zuba su a wasu bangarorin, ba komai bane face rusa kai.

KU KARANTA: Hukumar tace fina finai ta sake kama Naziru Sarkin Waka

"Gwamnatin jihar Lagos da gwamnatin tarayya dole zasu yi amfani da kudaden da ya kamata ace an yi amfani da su a wasu bangarorin don gyara abubuwan da aka lalata."

Gwamnatin jihar Kaduna ta kuma jajantawa rundunar yan sandan Najeriya da kuma wanda suka rasa iyalan Su sanadiyar rikicin, kuma gwamnatin tarayya ba zata sake barin irin wannan abu ya kara faruwa ba.

A nasa bangaren, Sanwo-Olu ya godewa abokin nasa, yace jahar ta fara matsawa gaba amma "Ba muji dadin yadda wasu suka sa jahar tayi rashin dadi ba, wanda wasu masu zuciyar tada fitina suka lalata tattalin arzikin jahar mu da kuma gadon mu ba."

A wani labarin, hukumar Kula da Cinkoson Ababen Hawa na Jihar Kano ta sanar da cewa tana shirin daukan sabbin ma'aikata a kalla 700 don kara wa kan 2,500 da ta ke da su a jihar a halin yanzu.

Shugaban na KAROTA, Baffa Dan'agundi ne ya sanar da hakan yayin da ya ke zantawa da 'yan jarida a ranar Laraba a jihar Kano.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel