Alkali ya bada belin Naziru Sarkin Waƙa
- Hukumar tace fina finai ce ta gurfanar da mawaki Naziru Ahmad bisa zargin sakin wakokin da ba'a tace ba
- Naziru Sarkin Waka ya musanta zargin, sai dai kotu ta sanya sabuwar rana don ci gaba da sauraren karar
- Ana ganin cewa mawakin ya soki gwamnan Kano Abdullahi Ganduje a cikin wasu wakoki biyu
Alkalin wata kotun Majistare ya bada shahararren mawaki Naziru Ahmad (Sarkin Waka), a hannun beli akan mutane biyu zasu tsaya masa da kuma kudi naira miliyan daya.
Hukumar tace fina-finai ce ta kama Naziru bisa zargin sakin wasu wakoki biyu "Gidan Sarauta" da kuma "Sai Hakuri".
DUBA WANNAN: Wani mutum ya yi barazanar kai coci kotu idan bata biya shi kuɗin baikonsa na shekaru 19 ba
Alkalin kotun, Aminu Gabari ya bada belin mawakin bisa sharadin zai gabatar da mutane biyu da zasu tsaya masa kuma dole daya ya kasance mahaifinsa ko dan uwansa, dayan kuma dole ya kasance Wakilin Gabas, Arewa ko Kudu a Kano, ko kuma daya daga kwamandojin Hisba a kananan hukumomi 44 da ke jihar.
Gabari ya kuma ce dukkan wanda zasu tsaya masa dole sai sun mika "fasfo dinsu na fita kasashen waje".
KU KARANTA: 'Yan shi'a sun ƙona tutar Faransa a Abuja kan kalaman shugaban Faransa, Macron
Tunda farko, Lauyan masu karar ya ce a ranar 12 ga Satumbar 2019 ne mawakin ya aikata laifin, laifin daya sabawa sashe 112 na dokar hukumar tace fina-finai shekarar 2001.
Barista Wada Ya ce an dawo da shari'ar ne daga wata kotun Majistire dake zamanta a Rijiyar Zaki zuwa inda aka bada belin nasa a Nomansland.
Ya kuma bukaci kotun da saka rana don bashi damar gabatar da hujjoji.
Wanda ake karar Naziru Sarkin Waka, bai amsa laifin ba kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Kotun ta bada shi a hannun beli ta kuma sanya ranar daya ga watan Disamba don ci gaba da sauraren karar.
Sai dai, an gano cewa a cikin wakokin biyu mawakin ya soki gwamnan Kano Abdullahi Ganduje.
A wani labarin daban, fusatattun matasa a garin Daudu a ƙaramar hukumar Gina, a ranar Talata, sun ƙona Divine Shadow Church kan alaƙanta mai cocin da satar mazakuta a garin kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Kwana ki uku da suka shuɗe, matasan sun yi zanga zanga a babban titin Makurdi - Lafia kan abinda suka kira 'batar mazakutar' mutum shida cikin wata guda a garin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng