Hukumar tace fina finai ta sake kama Naziru Sarkin Waka

Hukumar tace fina finai ta sake kama Naziru Sarkin Waka

- Hukumar tace fina finai ce ta gurfanar da mawakin bisa zargin sakin wakokin da ba'a tace ba

- Hakan na zuwa ne bayan gurfanar da shi da aka yi a kotu inda ya musanta laifin da ake zarginsa da aikatawa

- Ana ganin cewa mawakin ya soki gwamnan Kano Abdullahi Ganduje a cikin wakokin

Hukumar tace fina finai ta Jihar Kano ta sake kama fitaccen Mawaki Naziru M Ahmad, wanda aka fi sani da sani da Sarkin Waka.

Mawakin, wanda tsohon sarkin Kano Sunusi ya nada mukamin sarkin waka, an kama shi da fari tun Satumbar waccan shekarar 2019, bayan ya saki wakar da ke sukar Gwamna Abdullahi Ganduje.

Shahararren mai shiryawa da bada umarni a masana'antar Kannywood, Mal. Aminu Saira ne ya wallafa a shafinsa na Tuwita da daren ranar Laraba.

Hukumar tace fina finai ta sake kama Naziru Sarkin Waka
Hukumar tace fina finai ta sake kama Naziru Sarkin Waka. Hoto: @daily_nigerian
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Wani mutum ya yi barazanar kai coci kotu idan bata biya shi kuɗin baikonsa na shekaru 19 ba

Ya wallafa a shafin nasa: "Ina mai alhinin sanar da yan uwa da abokan arziki cewa hukumar Tace fina-finai karkashi Gwamnatin Jihar Kano ta sake kama dan uwana Naziru M. Ahmad. (Sarkin waka) A yanzu haka yana tsare. Karin bayani na nan tafe."

Sai dai an gaza jin ta bakin shugaban hukumar Ismaila Afakalla.

DUBA WANNAN: Mattacen ɗan takara da korona ta kashe ya ci zaben majalisa a Amurka

A baya bayan nan ne dai wata kotun majastire dake zamanta a Nomansland ta saurari karar da aka shigar da sarkin wakar bisa zargin fitar da wasu wakoki da ba'a tantance ba, "Gidan Sarauta" da "Sai hakuri" ranar 12 ga Satumbar 2019.

Sai dai mawakin ya musanta zargin daya sabawa sashe na 100(2) kuma aka tanadi hukuncin sa a sashe na 112 a dokar hukumar tace fina finai ta 2001.

Alkalin kotun, Aminu Gabari ya bada belin mawakin bisa sharadin zai gabatar da mutane biyu da zasu tsaya masa kuma dole daya ya kasance mahaifinsa ko dan uwansa, dayan kuma dole ya kasance mai sarautar gargajiya a yankin sa, ko kuma daya daga kwamandojin Hisba a kananan hukumomi 44 da ke jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel