'Yan sanda da aka kashe sanadiyyar zanga-zanga za su samu karin matsayi - IGP

'Yan sanda da aka kashe sanadiyyar zanga-zanga za su samu karin matsayi - IGP

- Jami'an rundunar 'yan sanda da dama sun rasa rayukansu a rikicin da ya barke sakamakon zanga-zanagr ENDSARS

- Babban sifeton rundunar 'yan sanda IGP, Mohammed Adamu, ya zagaya jihohi domin ganin irin barna da ta'adin da aka yi wa rundunar 'yan sanda

A wani yunƙurin ƙarawa jami'an ƴansanda himma da karsashi a ƙasa baki ɗaya domin farfaɗowa da sauri daga illolin zanga-zangar #EndSARS, babban Sufetan ƴansanda na ƙasa ya ce dukkanin jami'an da suka rasa ransu ko suka jikkata za'a ɗaga darajarsu zuwa matsayi na gaba .

Da ya ke magana a ranar Laraba, IGP Mohammed Adamu ya tabbatar cewa da jami'an zasu cigaba da morar inshorar lafiya dasu da iyalansu koda kuwa bayan sun bar aikin su ne.

Ya ce shugabancin hukumar yansanda na aiki da hukumar kula da ƴansanda don ganin an kawo sabon sauyi a rundunar ƴansandan Najeriya.

IGP Adamu ya bayyana hakan a Jihar Benin jim kaɗan bayan duba irin ɓarnar da zanga-zangar #EndSARS ta haifar inda ya kai ziyara ofisoshin ƴansanda da aka ƙona ko aka lalata su tare da motocin ƴansandan na fita aiki.

KARANTA: Taron gwamnoni da sarakunan arewa abin kunya ne ga yankin - CNG ta yi caccaka

Ya kai ziyara asibitin koyarwa na jami'ar Benin inda anan ne ake kula da jami'an ƴansandan da suka jikkata.

Yayin gabatar da jawabi ga jami'an rundunar tasa a hedikwatar ƴansanda a birnin Benin, Adamu ya samu rakiyar mataimakin gwamnan jihar, Comrade Philip Shaibu, wanda ya wakilci gwamna Godwin Obaseki.

'Yan sanda da aka kashe sanadiyyar zanga-zanga za su samu karin matsayi - IGP
IGP Mohammed Adamu
Asali: Twitter

"Lokacin da muke bakin aiki muna samun inshorar lafiya, amma da zarar mun bar bakin aiki shikenan ta tsaya."

"Yanzu wannan gwamnatin tace a'a, ba'a ƙarfafa muku guiwa ba in akayi hakan, yanzu ya zama doka koda jami'i ya bar bakin aikinsa zai cigaba da morar tsarin inshorar lafiya," a cewar IGP Adamu

Ya ƙara da cewa; "a halin yanzu, sama da jami'ai 60,000 da suka bar aiki an maida su cikin tsarin inshorar.

"Muna basu karfin gwuiwar su zo ba tare da wata fargaba ba don cin moriyar tsarin inshorar gwamnati.

"An saka hannu a sababbin tsare-tsaren da zasu kula da walwala da jin daɗin jami'an ƴansanda."

A cigaba da jawabinsa Adamu yace, "za'a biya diyya ga iyalan jami'an da suka ransu da waɗanda suka jikkata sakamakon zanfa-zangar #EndSARS."

Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta ƙara albashin jami'ai da kaso mai tsoka don ƙarfafa musu guiwar gudanar da ayyukan su.

KARANTA: Magidanci ya yi garkuwa da diyarsa a Kano, ya bukaci matarsa ta biya N2m kudin fansa

"Ba mu buƙatar barin ayyukan mu don bawa masu laifi gurbi ko damar cin karen su babu babbaka" ya faɗi hakan lokacin da yake jinjinawa da yabawa jami'an duk da ƙalubalen da suke fuskanta.

Mataimakin gwamnan yace gwamnatin su zata cigaba da tallafawa rundunar ƴansanda din gudanar da ayyukan su.

"Gwamna Godwin Obaseki tuni ya sahale a sake gina ofisoshin da aka lalata da suke bukatar gyara." a cewarsa.

A ranar Laraba ne Legit.ng Hausa ta wallafa cewa haɗakar ƙungiyoyin Arewa (CNG) ta bayyana taron da ya wakana baya-baya nan tsakanin ƙungiyar gwamnonin Arewa (NGF) da Sarakunan gargajiya a matsayin abin kunya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel