Gwamna Masari ya ce gwamnatinsa ta dena yin sulhu da 'yan bindiga

Gwamna Masari ya ce gwamnatinsa ta dena yin sulhu da 'yan bindiga

- Aminu Bello Masari, gwamnan jihar Katsina ya ce gwamnatinsa ba za ta sake yin sulhu da 'yan bindiga ba

- Gwamnan ya yi wannan jawabin ne yayin da hukumomin tsaro suka gudanar masa da wasu tubabban shugaban 'yan bindiga

- Masari ya yi kira ga hukumomin tsaro su zage damtse wurin ganin sun taka wa 'yan bindigan birki tare da kawo karshensu

Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina ya bayyana cewa gwamnatinsa ba zata yi sulhu da 'yan ta'addan da ke addabar jihar dama makota ba kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Saboda da haka ya umarci shugabanni da su dauki mataki mai tsanani akan yan bindiga, wanda, acewarsa, su ne masu garkuwa da mutane don a biya kudin fansa, fyade, kona dukiyar al'umma da kuma satar shanu.

Babu batun sake sulhu da 'yan bindiga - Gwamna Masari
Babu batun sake sulhu da 'yan bindiga - Gwamna Masari. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Zaɓen Amurka: Magoya bayan Trump sunyi zanga-zanga a ofishin ƙidayar ƙuri'u ta Arizona

A wata sanarwa da daraktan yada labarai, Abdu Labaran Malumfashi, ya fitar, ya ce gwamnan ya yi magana jiya yayin da shugabannin tsaro suka gabatar masa da wasu kwamandojin 'yan bindiga da suka tuba, suka kuma dawo da bindigu 10 kirar AK 47.

"Na umarci jami'an tsaro da su dauki mataki mai tsauri akan yan tawayen har sai an kawo karshen su.

"Baza mu sake sulhu dasu ba, amma, idan bisa ra'ayin kansu, suka yanke shawarar daina ayyukan ta'addancin suka kuma rungumi zaman lafiya, a shirye muke mu saurare su.

"Kuma ko hakan ne, dole sai sun mika makamansu da sauran kayan ta'addancin, ko kuma su ci gaba da zama makiya da za a hukunta, matukar muna raye.

"Gwamnati a shirye take ta karbi tuba ta kuma tallafawa yan bindigan, matukar suka mika makamansu da kayayyakin ta'addancin da suka mallaka, amma mu ba wanda zamu lallaba," kamar yadda gwamnan yake fadi.

KU KARANTA: Mattacen ɗan takara da korona ta kashe ya ci zaben majalisa a Amurka

Shugabannin yan tawayen, Sale Turwa da Muhammad Sani Maidaji, sune wanda aka gabatarwa da gwamnan ta hannun Kwamishinan yan sandan jihar Katsina, Sunusi Buba, da abokan aikinsa daga hukumar Civil Defense.

Gwamna Masari ya ce jami'an tsaro su ci gaba da zage damtse wajen yakar 'yan tada kayar baya har sai an kawo karshen ayyukansu.

A wani labarin, hukumar Kula da Cinkoson Ababen Hawa na Jihar Kano ta sanar da cewa tana shirin daukan sabbin ma'aikata a kalla 700 don kara wa kan 2,500 da ta ke da su a jihar a halin yanzu.

Shugaban na KAROTA, Baffa Dan'agundi ne ya sanar da hakan yayin da ya ke zantawa da 'yan jarida a ranar Laraba a jihar Kano.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel