Maimakon raguwa, adadin masu kamuwa da Korona ya fara karuwa a Najeriya

Maimakon raguwa, adadin masu kamuwa da Korona ya fara karuwa a Najeriya

- Maimakon samun sauki, daruruwan yan Najeriya na sake kamuwa da cutar Korona

- Gwamnatin tarayya na tsoron adadin masu kamuwa da cutar zai yi tashin gwauron zabi sakamakon zanga-zangar ENDSARS

Najeriya ta samu adadin sabbin masu cutar Coronavirus 155 ranar Laraba a cewar hukumomin kiwon lafiya.

Adadin da aka samu ranar Laraba ya kai jimillan wadanda suka kamu da cutar 63,328 a Najeriya.

Hukumar hana yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta sanar da hakan a daren Laraba , 5 ga watan Nuwamba, 2020.

Yayinda adadin masu kamuwa ke raguwa, adadin masu samun waraka daga cutar na kara yawa.

Daga cikin mutane sama da 63,000 da suka kamu, an sallami 59,675 yayinda 1155 suka rigamu gidan gaskiya.

DUBA NAN: Hukumar tace fina finai ta sake kama Naziru Sarkin Waka

Jerin jihohi da Sabbin mutanen da suka kamu –

Lagos-85

FCT-23

Ondo-18

Ogun-8

Kaduna-5

Oyo-5

Taraba-5

Kano-3

Rivers-2

Bauchi-1

KAI TSAYE: Sakamakon zaben kasar Amurka sun fara fitowa, Trump 214, Biden 248

Maimakon raguwa, adadin masu kamuwa da Korona ya fara raguwa a Najeriya
Maimakon raguwa, adadin masu kamuwa da Korona ya fara raguwa a Najeriya Credit: @NCDCGov
Asali: Twitter

A bangare guda, Dirakta Janar na hukumar lafiyar duniya (WHO) Tedros Ghebreyesus Adhanom, ya shiga killace kansa bayan haduwa da wani tabbataccen mai cutar Coronavirus.

Ya sanar da hakan a shafinsa ta Tuwita @Dr.Tedros.

A cewarsa: "An gano na hadu da wani mutum mai alamun cutar COVID-19, ina cikin koshin lafiya kuma babu wasu alamu tattare dani amma zan killace kaina na tsawon kwanaki masu zuwa a gida."

"Ni da abokaina a WHO zamu cigaba da tattaunawa da abokan hulda domin ceton rayukan marasa galihu,"

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel