Muna kokarin hana sake barkewar zanga-zangar EndSARS a karo na biyu – Shugaban gwamnonin Arewa

Muna kokarin hana sake barkewar zanga-zangar EndSARS a karo na biyu – Shugaban gwamnonin Arewa

- Kungiyar gwamnonin Arewa sun bayyana kokarin da suke yi na dakile yiwuwar barkewar zanga-zangar EndSARS a karo na biyu

- Simon Lalong wanda shine shugaban kungiyar ya ce suna shirin fara tattaunawa da matasa a kan haka

- Ya ce babu laifi gudanar da zanga-zangar amma wasu bata gari ne suka janye ragamar gangamin

Shugaban kungiyar gwamnonin Arewa, Simon Lalong, ya bayyana cewa suna kokarin tattaunawa da matasan Najeriya da kuma kokarin hana barkewar zanga-zangar EndSARS a karo na biyu.

Lalong wanda ya kuma kasance gwamnan jihar Filato ya bayyana hakan ne a wata hira da Channels Television a ranar Litinin, 2 ga watan Nuwamba.

Ya ce an yanke shawarar hana sake afkuwar zanga-zangar EndSARS ne bayan wata ganawa da dattawan arewa ciki harda gwamnoni, sarakunan gargajiya, da shugabannnin siyasa a arewa suka yi.

KU KARANTA KUMA: Ragewa iyaye kudin makaranta: Gwamnatin Kano ta kafa kwamiti kan haka

Muna kokarin hana sake barkewar zanga-zangar EndSARS a karo na biyu – Shugaban gwamnonin Arewa
Muna kokarin hana sake barkewar zanga-zangar EndSARS a karo na biyu – Shugaban gwamnonin Arewa Hoto: @SimonLalong
Asali: Twitter

“Mun fito daga taron cike da shawarwari masu amfani.

“A wannan taron, duk mun amince da komawa da kuma ci gaba da tattaunawa musamman don magance lamura daga EndSARS saboda muma muna kokarin hana sake barkewar EndSARS a karo na biyu.

“Muna so mu magance wasu daga cikin matsalolin da ke kasa, domin hana mutane yin barna. Saboda bata gari sun janye zanga-zangar wanda ya yi sanadiyar barna da dama,” in ji shi.

Lalong ya ce koda dai babu laifi a zanga-zangar EndSARS, amma dai wasu masu neman sauyin gwamnati sun janye ragamar gangamin.

KU KARANTA KUMA: Allah ka hanemu da taurin kai, izza da jin babu wanda ya isa ya fada mana mu ji – Ali Nuhu

A gefe guda, Shugabar hukumar kula da yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa, a jiya Litinin, 2 ga watan Nuwamba, ta bayyana cewa za a dawo da bakwai daga cikin yan Najeriya takwas da suka gudanar da zanga-zangar EndSARS a Masar.

A wasu jerin wallafa da tayi a shafin Twitter, Dabiri-Erewa ta ce bayan kamunsu, sun roki hukumar da ta sanya baki sannan ta tabbatar da sakinsu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng