Fatakwal: An kama manyan jagororin IPOB 2 biyo bayan kashe-kashe a Oyigbo - Wike

Fatakwal: An kama manyan jagororin IPOB 2 biyo bayan kashe-kashe a Oyigbo - Wike

- Nyeson Wike, gwamnan jihar Ribas, ya ce an kama wasu manyan jagororin haramtacciyar kungiyar IPOB guda biyu

- Ana zargin jagororin biyu da hannu a cikin rikicin da ya barke a yankin Oyigbo da ke Fatakwal

- A cewar Wike, 'yan ta'addar kungiyar IPOB sun yi amfani da zanga-zangar lumana ta ENDSARS a Fatakwal domin tayar da zaune tsaye

Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, a ranar talata, ya ce jami'an tsaro sun sami nasarar kama biyu daga cikin ƙasurguman yan ta'adda na haramataciyyar ƙungiyar fafutikar kafa ƙasar Biyafara (IPOB).

A cewarsa, waɗanda aka kama din na da hannu dumu-dumu wajen kisan gilla ga sojoji shida 6 da ƴan sanda huɗu 4 a Oyigbo.

Wike ya jaddada cewa matakin da ya ɗauka na saka dokar ta ɓaci ya taimaka matuƙa wurin hana afkuwar rikici tsakanin al-ummar Hausawa da Igbo.

An kama waɗanda ake zargin a yammacin Ranar Litinin.

Gwamna Wike yace an gudanar da zanga-zangar #EndSARS ta lumana a jiharsa kafin masu aikata laifi a ƙarƙashin ƙungiyar IPOB su shiga cikin zanga-zangar.

KARANTA: Zaben shugaban kasar Amurka: An saka dokar ta baci a jihar Oregon

Gwamnan ya ce ƴan ƙungiyar IPOB ne suke son shafawa jihar kashin kaji ta hanyar kashe jami'an tsaro goma a Oyigbo.

Fatakwal: An kama manyan jagororin IPOB 2 biyo bayan kashe-kashe a Oyigbo - Wike
Gwamna Nyesom Wike @Thecable
Asali: UGC

Jihar Rivers gida ne na kowanne addini da ƙabila,wasu ɓatattun ƴan ƙungiyar IPOB suke son tada zaune tsaye a Oyigbo ta hanyar ƙirƙirar faɗan ƙabilanci a tsakanin Hausawa da 'yan kabilar Igbo.

KARANTA: IGP Adamu ya nada AIG Dandaura da AIG Adamu Alkali su shugabanci wasu bangare a NPF

Ya ce "ba don mun yi saurin ɗaukar mataki a Oyigbo ba, da ba'a san matakin da rikicin zai kai ba daga baya."

Gwamnan ya ce duk da bashi da kyakkyawar alaƙa da rundunar sojin da ƴansandan Najeriya, ba zai lamunci kashe jami'in soja ko ɗan sanda a jiharsa ba.

"Ba zan goyi bayan aikata laifi ba. Ba zai yiwu don sojoji basa sona kuje ku kashe su ba.

''Ni kuma kawai sai na goyi bayanku, na ce kunyi dai-dai, hakan sam ba zai yiwu ba ace na zo domin yi muku godiya bisa ɓarna," a cewar Wike.

Ko a karshen makon jiya sai da Wike ya bayyana cewa tsagerun mambobin kungiyar IPOB sun kashe sojoji da 'yan sanda a Fatakwal, kamar yadda Legit.ng ta rawaito.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel