IGP Adamu ya nada AIG Dandaura da AIG Adamu Alkali su shugabanci wasu bangare a NPF

IGP Adamu ya nada AIG Dandaura da AIG Adamu Alkali su shugabanci wasu bangare a NPF

- Babban sifeton rundunar 'yan sanda (IGP) ya nada sabbin shugabanni da zasu shugabanci wasu bangarori biyu na 'yan sanda

- Kazalika, IGP ya nada sabon sakataren rundunar 'yan sanda

- A cewar kakakin rundunar 'yan sanda, DCP Frank Mba, an yi sabbin nade-naden ne biyo bayan ritayar tsofin shugabannin sashen

Babban sifeton rundunar 'yan sanda (IGP), Mohammed Adamu, ya amince da nadin DIG Sanusi N. Lemu, da AIG Usman Alkali Baba, a matsayin shugabannin sashen atisaye da sashen kudi da gudanarwa na rundunar 'yan sanda.

A cikin wani jawabi da kakakin rundunar 'yan sanda, DCP Frank Mba, ya fitar ranar Talata, ya ce an yi sabbn nade-naden ne biyo bayan ritayar tsofin shugabannin sashen; DIG Abdulmajid Ali da AIG Abduldahiru Danwawu, wadanda wa'adin shekarunsu na aiki ya cika.

DCP Mba ya bayyana cewa IGP Adamu ya amince da nadin AIG Mustapha Dandaura amatsayin sakataren rundunar 'yan sanda kuma mamba a tawagar gudanarwa ta rundunar 'yan sanda.

"Sabon shugaban sashen atisaye, DIG Sanusi Lemu, mni, kwararren dan sanda ne da yake da shaidar karatun digiri BA(Ed) a kimiyyar siyasa. Ya halarci kwasa-kwasai daban-daban da suka bashi tarin ilimi a bangaren gudanar da aiki.

"AIG Usman Alkali Baba, psc (+), fdc, jazirtaccen dan sanda ne da ke da shaidar kammala karatun gaba da digiri a bangaren sanin gudanar da aiki (MPA) da kuma shaidar kammala digiri na farko a bangaren kimiyyar siyasa BA(Ed). Shi ma ya halarci kwasa-kwasai da dama tare da samun horo kala-kala a bangaren tafiyar da aiki.

KARANTA: Ke mayya ce idan mijinki ya tsiyace bayan kun yi aure - Malamar Mata

"Dan asalin jihar Yobe, AIG Baba ya rike muhimman mukamai a rundunar 'yan sanda wadanda suka hada da; AIG a shiyya ta 5 da ke Benin, shiyya ta 4 da ke Makurdi, da kuma shiyya ta 7 da ke Abuja.

IGP Adamu ya nada AIG Dandaura da AIG Adamu Alkali su shugabanci wasu bangare a NPF
AIG Dandaura da AIG Adamu Alkali @TheNation
Asali: Twitter

"Ya rike mukamin kwamishinan 'yan sanda a Abuja da Delta da sauransu. AIG Baba ya na rike da mukamin sakataren rundunar 'yan sanda kafin sabon nadinsa a matsayin mukaddashin shugaba mai kula da bangaren kudi da gudanar da aiki.

KARANTA: Najeriya ta ƙara faɗawa tsilla-tsilla sakamakon sake faɗuwar farashin ɗanyen man fetur

"Kazalika, IGP ya amince da nadin AIG Mustapha Dandaura a matsayin sabon sakataren rundunar 'yan sanda kuma mamba a tawagar gudanarwa ta rundunar 'yan sanda, zai karbi aiki daga hannun AIG Alkali Baba.

"AIG Dandaura ya fara aikin dan sanda a ranar 3 ga watan Maris na shekarar 1990 bayan ya kammala karatun digiri na farko a bangaren tarihi a jami'ar BUK.

"Kafin nadinsa a matsayin sakataren rundunar 'yan sanda, AIG Dandaura ya na rike da mukamin babban mai tsawatarwa a hedikwatar rundunar 'yan sanda ta kasa da ke Abuja. A baya ya taba rike mukamin kwamishinan 'yan sanda a jihar Ribas da Anambra," a cewar DCP Mba.

A karrshen makon jiya ne Legit.ng Hausa ta wallafa rahoton cewa 'yan sanda a ƙasar Italiya sun kama mutum saba'in da da uku (73) ƴan ƙungiyar matsafa kuma ƴan asalin Najeriya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel