Buhari ya zagaye kansa da 'yan iska masu sharara masa karya - Father Mbaka
- Duk da soyayyan da yake wa Buhari, Fada Mbaka ya yiwa shugaban kasan wankin babban bargo
- Mbaka ya ce Buhari bai da masu fada masa gaskiyar halin da yan Najeriya ke ciki
- Ya zargi jami'an tsaro da kashe masu zanga-zangar EndSARS a Enugu
Babban faston cocin Adoration Ministry, Rabaran Ejike Mbaka, ya zargi shugaba Muhammadu Buhari da zagaye kansa da yan iska da bata gari.
Mbaka ya ce wadannan yan iskan da Buhari ya zagaye kansa dasu suna sharara masa karya kan ainihin halin da yan Najeriya ke ciki.
A cewar PUNCH, Faston ya bayyana hakan ne a taron ibadar ranar Lahadi.
Ya bukaci Buhari ya baiwa yan Najeriya hakuri, musamman matasa. kan irin halin kuncin da aka sanyasu.
Mbaka ya tuhumci jami'an tsaro a jihar Enugu da laifin kisan masu zanga-zangar EndSARS sannan suka jefa gawawwakinsu kan tsaunin Onyeama.
Ya ce yanzu haka an garkame matasa da yawa a kurkuku a fadin tarayya.
Mbaka ya kara da cewa a daina kisa da daure matasan yankin Biafra.
KU KARANTA: Dakarun soji sun halaka 'yan Boko Haram 75, sun rasa sojoji 3 a Borno
KU KARANTA: Yadda zaben kasar Amurka ke gudana tsakanin Trump da Biden
"Wannan ba maganan EndSARS ko IPOB bane. Babu wanda ke yaki da wannan gwamnatin; da rashin shugabancin kwarai muke yaki, " yace
"Kwanakin baya a tsaunin Miliken, bayan sabon kasuwa (dake Enugu), an ga gawawwakin wadanda aka harba kuma aka kashe yayin zanga-zanga. Sun jefar da gawawwakin mutane yayinda iyalansu ke nemansu."
"Shin kuna tunanin wadannan matasan zasu zuba ido wadannan shugabannin su cigaba satan kudin al'umma ba."
"Buharin da ya kamata ya zama mafita, ya zagaye kansa da 'yan iska. Kawai karya suke fada masa." Ya kara
A wani labarin daban, a ranar majalisar dattawa ta shake ministan yada labarai, Lai Mohammed a dalilin wata kwangila.
Ma’aikatar yada labarai ta cusa wata kwangila ‘ERPG 10145116’ a kasafin kudin shekarar 2020 wanda gwamnatin tarayya ta dauki nauyin aikin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng