Dakarun soji sun halaka 'yan Boko Haram 75, sun rasa sojoji 3 a Borno

Dakarun soji sun halaka 'yan Boko Haram 75, sun rasa sojoji 3 a Borno

- Tun bayan kirkirar rundunar Operation FIRE BALL, mataimakiyar Operation LAFIYA DOLE ake ta samun nasara a Borno

- Cikin kankanin lokaci suka samu nasarar kashe 'yan Boko Haram 75, sai dai sojoji 3 sun rasa rayukansu, yayin da 4 suka samu raunuka

- Sojoji 4 da suka samu raunukan suna asibitin sojoji, kuma da alama kwalliya tana biyan kudin sabulu don suna samun sauki

Rundunar Operation Lafiya Dole tace mutane 78 duk da sojoji 3 suka rasa rayukansu a Borno, Dailytrust ta wallafa.

A wata takarda da kakakin rundunar soji, birgediya janar Benard Onyeuko ya saki a ranar Talata ya ce sun samu nasarar kashe 'yan ta'adda masu yawa a jihar.

Kamar yadda takardar tazo, "Tunda rundunar Operation FIRE BALL, mai taimakon Operation LAFIYA DOLE ta fara aiki, aka yi ta samun nasarori daban-daban a bangaren arewa maso gabas a kan miyagun 'yan ta'addan nan na Boko Haram.

"Rundunar suna cigaba da gudanar da ayyukan babu dare ba rana. Ba don sadaukarwa da jajircewar sojojinmu ba da ba za a samu wadannan nasarorin ba."

Dakarun soji sun halaka 'yan Boko Haram 75, sun rasa sojoji 3 a Borno
Dakarun soji sun halaka 'yan Boko Haram 75, sun rasa sojoji 3 a Borno. Hoto daga @Dailytrust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Gwamnonin Arewa sun sha alwashin tabbatar da hadin kan Najeriya

A cewarsa, yanzu haka an samu nasarar kashe 'yan Boko Haram 75 cikin dan kankanin lokaci.

An samu nasarar kwato bindigogi 6, injinan gyaran bindigogi 4, bindiga kirar PKT daya, kananan bindigogi 10, abubuwa masu fashewa, bindigogi masu jigida da sauran miyagun makamai daga hannayensu.

KU KARANTA: Ni mai kare martabar addini da Annabi ne a duk inda nake - Rahama Sadau ta yi martani a kan wani tsokaci

Sai dai kananan sojoji 2 da wani babban soja sun rasa rayukansu, yayin da wasu 4 suka samu miyagun raunuka.

Sojojin da suka samu raunukan na asibitin sojoji, inda ake kula da lafiyarsu kuma alamu na nuna kwalliya zata biya kudin sabulu.

A wani labari na daban, Ministan labarai da al'adu, Alhaji Lai Mohammed ya bayyana yadda shugaba kasa Muhammadu Buhari yake kokarin samar wa matasa ayyukan yi, wanda ba a taba yin hakan ba a tarihin Najeriya.

A wani taron da gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya jagoranta a Kaduna, wanda shugabanni da manyan mutane da dama suka samu damar halarta, Mohammed ya sanar da shirin da shugaban kasar ya fara.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel