Ku bayyana dukiyoyinku ko ku fuskanci hukuncin doka - Gwamna Sule ya sako ma'aikata a gaba

Ku bayyana dukiyoyinku ko ku fuskanci hukuncin doka - Gwamna Sule ya sako ma'aikata a gaba

- Doka ta wajabtawa ma'aikatan gwamnati da masu rike da mukamai suke bayyana dukiyoyinsu kowacce shekara

- An kirkira wannan doka ne domin dakile cin hanci ta hanyar bin diddigin hanyoyin da ma'aikaci ko jagora ke samun kudi

- Sai dai, rahotanni na yawan sanar da yadda ma'aikata da shugabanni ke yin funfurus tare da kin bayar da bayanan kadarorinsu

Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya umarci ma'aikatan gwamnati da su bayyana dukiyoyin su ko su fuskanci fushin kuliya dai-dai da hukuncin da aka tanadarwa ma'aikata masu ƙin bayyana dukiyoyinsu.

Ya bada umarnin ne lokacin taron sanin makamar aiki a kan bin dokar bayyana adadin dukiyar ma'aikatan gwamnati da kuma kundin dokar ma'aikatan gwamnati wanda sashen kula da dokokin ma'aikata ya shirya.

Yace taron yana yana da matukar muhimmanci kuma ya zo akan gaɓa, dai-dai lokacin da ake bukatarsa.

KARANTA: Najeriya ta ƙara faɗawa tsilla-tsilla sakamakon faɗuwar farashin ɗanyen man fetur

''Taron zai ƙarawa ma'aikata karsashi da zummar gaskiya yayin gudanar da ayyukansu.

Ku bayyana dukiyoyinku ko ku fuskanci hukuncin doka - Gwamna Sule ya sako ma'aikata a gaba
Gwamna Abdullahi Sule @Thecable
Asali: Twitter

"Ya zama dole kowanne ma'aikaci ya bayyana abin da ya mallaka," kamar yadda ya bayyana.

A cewarsa, hakan zai bawa gwamnatinsa damar kawar da dukkan wata almundahana da kuma kula da kuɗaɗen gwamnati yadda ya kamata.

KARANTA: IGP Adamu ya nada AIG Dandaura da AIG Adamu Alkali su shugabanci wasu bangare a NPF

"Ba zamu bar yunƙurin kare baitul mali ya tashi a banza ba. Ya zama wajibi akanmu mu jawo hankalin mutane cikin kakkausar murya akan tanadin da aka yiwa masu kin bin wannan doka da ke cikin kundin dokar ɗa'ar ma'aikata mai lamba CAP 15 LFM 2004.

"Muna umartar Dukkan ma'aikatan gwamnati su bi wannan dokar, su bayyana dukiyoyin su kamar yadda doka ta tanada don kaucewa fushin hukuma"

Gwamnan ya ƙara da cewa "Manufar kundin ɗa'ar ma'aikata shine ɗabbaƙa gaskiya, adalci, da aiki tuƙuru. Manufar tsarin ta yi dai-dai da manufar gwamnatinmu.''

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel