COVID-19: Firaministan UAE ya sadaukar da kansa domin gwajin allurar rigakafin Korona da likitocin kasar suka kirkira

COVID-19: Firaministan UAE ya sadaukar da kansa domin gwajin allurar rigakafin Korona da likitocin kasar suka kirkira

- Sheikh Mohmmed bin Rashid Al Maktoum, firaministan haddadiyar daular Larabawa (UAE) ya sake bawa duniya mamaki

- A wannan karon, Al Maktoum ya sadaukar da kansa ne domin gwajin allurar rigakafin cutar korona

- Al Maktoum bai bayyana cewa ya na dauke da kawayar cutar korona ba ko kuma hukumar lafiya ta duniya ta amince da allurar rigakafin ba

Firaministan haɗaɗɗiyar daular larabawa, Sheikh Mohammed bin Rashid Al Maktoum,ya bayyana cewa an yi masa gwajin allurar rigafin cutar korona wadda jami'an lafiyar UAE suka ƙirƙira.

Ya wallafa hotonsa a shafinsa na tiwita lokacin da likitansa ke tsaka da yi masa allurar rigakafin.

Ya jinjinawa jami'an lafiyar kasar UAE bisa aiki tuƙuru wajen samar da allurar rigakafin.

DUBA WANNAN: IGP Adamu ya nada AIG Dandaura da AIG Adamu Alkali su shugabanci wasu bangare a NPF

Sai dai, har yanzu bai bayyana ko allurar rigakafin ta samu sahalewar hukumar lafiya ta duniya ba.

Kuma bai bayyana ko yana da cutar ko bashi da ita ba.

Firiministan ya rubuta a shafinsa na Tuwita, "a yayin da akayi min allurar rigakafin kamuwa da cutar korona a yau, ina yi wa kowa fatan samun ƙoshin lafiya.

COVID-19: Firaministan UAE ya sadaukar da kansa domin gwajin allurar rigakafin Korona da likitocin kasar suka kirkira
Sheikh Al Makhtoum @Thecable
Asali: Twitter

''Ina mai alfahari da likitocinmu wanda suka yi aiki tuƙuru don samar da allurar a wannan daular ta mu (UAE).

Makomar ƙasarmu a kodayaushe zata kasance kyakkyawa."

Ana bukatar allurar rigakafi cikin hanzari don kaucewa sake ɓallewar annobar Korona a karo na biyu.

DUBA WANNAN: Zaben shugaban kasa: Zan sake kafa tarihi a kasar Amurka - Trump ya cika baki

Ƙasashen turai da dama da suka haɗar da Faransa, Ingila, Jamani, Sifen da sauransu sun ƙara tsaurara matakai don daƙile yaɗuwar cutar.

Hakazalika, Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta ce zata fi baiwa waɗanda cutar ta shafa muhimmanci duk lokacin da aka samu allurar rigakafi mafi dacewa.

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, a satin da ya gabata ya sanar da cewa tattalin arziƙin Najeriya bashi da ƙwarin da zai iya jure dokar kulle a karo na biyu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng