Ragewa iyaye kudin makaranta: Gwamnatin Kano ta kafa kwamiti kan haka

Ragewa iyaye kudin makaranta: Gwamnatin Kano ta kafa kwamiti kan haka

- Gwamnatin Abdullahi Ganduje ta jihar Kano ta kafa kwamiti na musamman domin aiwatar da shirin zabgewa iyayen dalibai a jihar kudin makaranta

- Za a yi hakan ne domin rage masu radadin halin da suka riski kansu a ciki sakamakon annobar korona

- Kwamishinan ilimi na jihar Kano, Muhammad Sanusi Sa’idu Kiru ne ya bayyana hakan a taron manema labarai

Rahotanni sun kawo cewa gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Gandue, ta kafa wani kwamiti domin aiwatar da shirin ragewa iyayen dalibai a jihar kudin makaranta.

Gwamnatin na yunkurin zabtare kudin makarantar ne da kaso 25 cikin 100 sakamakon mawuyacin halin da annobar COVID-19 ta sanya mutane a ciki.

Sashin Hausa na BBC ya ruwaito cewa, kwamishinan ilimi na jihar Kano, Muhammad Sanusi Sa’idu Kiru ne ya sanar da hakan a wani taro na manema labarai.

Ragewa iyaye kudin makaranta: Gwamnatin Kano ta kafa kwamiti kan haka
Ragewa iyaye kudin makaranta: Gwamnatin Kano ta kafa kwamiti kan haka Hoto: @bbc
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Allah ka hanemu da taurin kai, izza da jin babu wanda ya isa ya fada mana mu ji – Ali Nuhu

A kwanakin baya ne aka fara samun sabani tsakanin gwamnatin jihar da masu makarantu masu zaman kansu, saboda bukatarta na ganin an ragewa iyaye kudin makarantar saboda annobar korona.

Su dai masu makarantun na cewa suma annobar ta shafe su, sannan basu da wata hanya ta biyan malaman da ke koyarwa albashinsu idan suka aiwatar da buƙatar gwamnatin.

Sai dai kwamishinan ilimi na jihar ya ce makarantu masu zaman kansu da dama a jihar sun fara aiwatar da sabon tsarin.

KU KARANTA KUMA: Kannywood: Babban darakta Falalu dorayi ya yi wa Rahama Sadau shagube a kan shigar da ta yi

A baya mun ji cewa Kiru ya umarci duk masu makarantu masu zaman kansu da su zabtare kudaden makaranta da kashi 25 bisa dari zuwa ranar 1 ga watan Nuwamba ko kuma ta hana biyan kudin makarantar zango na ukun shekarar 2020.

Kwamishinan ya fadi hakan ne a wata takarda da ya gabatar wa da jaridar Vanguard a ranar Alhamis.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng