Ku zabge kudin makaranta ko a soke zango na 3 na karatu - Gwamnatin Kano ga masu makarantun kudi

Ku zabge kudin makaranta ko a soke zango na 3 na karatu - Gwamnatin Kano ga masu makarantun kudi

- Kwamishinan ilimi na jihar Kano, Muhammad Sunusi Kiru ya umarci masu makarantu da yanke kudin makarantar zango na biyu da kashi 25 bisa 100

- Ya sanar da hakan ne a wata takarda da ya gabatar wa jaridar Vanguard, inda yace wajibi ne masu makarantun kudi su yi hakan kafin 1 ga watan Nuwamba

- Ya wajabta hakan ne don masu makarantun su yi karamci ga iyayen yaran kamar yadda suka mori karamci daga gwamnatin jihar Kano a lokacin kullen COVID-19

Kwamishinan ilimi na jihar Kano, Muhammad Sunusi Kiru ya umarci duk masu makarantu masu zaman kansu da su zabtare kudaden makaranta da kashi 25 bisa dari zuwa ranar 1 ga watan Nuwamba ko kuma ta hana biyan kudin makarantar zango na ukun shekarar 2020.

Kwamishinan ya fadi hakan ne a wata takarda da ya gabatar wa da jaridar Vanguard a ranar Alhamis.

A cewar Kiru, ya umarci makarantu masu zaman kansu da yin hakan ne don su yi karamci ga iyayen yara kamar yadda gwamnati tayi musu lokacin da suka shiga tsananin yayin zaman kullen COVID-19.

Ku zabge kudin makaranta ko a soke zango na 3 na karatu - Gwamnatin Kano ga masu makarantun kudi
Ku zabge kudin makaranta ko a soke zango na 3 na karatu - Gwamnatin Kano ga masu makarantun kudi. Hoto daga @Vanguardngr
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dan gidan fursuna da ya tsere ya kashe wanda ya bada shaida a kan shi a kotu

Kwamishinan sun hada kwamitin da za su tattauna da masu makarantun don samun matsaya. Domin matsawar masu makarantun suka amshi kudi, zasu hukunta su.

Kamar yadda takardar tazo: "Mun hada kwamiti biyu wadanda za su tattauna da masu makarantu masu zaman kansu don su rage kashi 25 cikin dari, kamar yadda kusan jihohi 4 zuwa 5 suka yi, ko kuma mu hana biyan kudin makarantar zango na uku na shekarar nan, wanda zai fara daga watan Janairun 2021.

"Yakamata masu makarantun kudi su gwada karamci a kan tallafin da gwamnati tayi musu, a kan mutanen kirkin Kano."

KU KARANTA: Mun shawo kan matsalar tsaro a yankin arewa maso yamma da tsakiya - Buhari

Idan har ba su yi hakan ba zuwa 1 ga watan Nuwamba, ma'aikatar ilimi za ta dauki matakin da suka dace a kan makarantun.

A wani labari na daban, wani rikici ya na ta ruruwa a masarautar Alade Idanre da ke jihar Ondo a kan wanda zai gaji Olusegun Akinbola, sarkin masarautar da ya rasu a ranar 16 ga watan OKtoba.

Bayan kwana biyu da rasuwar sarkin, an nada Temilowa Akinbola, diyarsa ta farko a matsayin sarauniyar rikon kwarya.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel