Jarumi Adam A. Zango ya yi addu'a mai ratsa zuciya ga Rahama Sadau

Jarumi Adam A. Zango ya yi addu'a mai ratsa zuciya ga Rahama Sadau

- Jarumi Adam A. Zango ya yi wa jaruma Rahama Sadau addu'o'in neman shiriya

- Jarumin ya yi wallafa a Instagram cike da alhinin batancin da hotunanta suka janyo

- Ya yi fatan Allah ya shiryata idan mai shiryuwa ce ko kuma ya la'anceta idan ta ki shiryuwa

Fitaccen jarumin Kannywood, Adam A. Zango, ya kwarara addu'o'i ga Rahama Sadau a kan batancin da aka yi wa manzon Allah a karkashin hotunan da ta wallafa.

Kamar yadda ake gani, wadannan hotunan sun matukar janyo cece-kuce da maganganu kala-kala daga jama'a daban-daban.

Daga cikin abinda ya sake tada hankulan jama'a shine wani tsokaci da daya daga cikin abokan jarumar ya yi a karkashin hotunan, lamarin da yasa ta fito ta barranta kanta daga tsokacin tare da nuna nadamarta.

A safiyar yau Talata ne jama'a da dama suka dinga raddi tare da dora dukkan laifin abinda ya faru a kan jarumar, ganin cewa sai bango ya tsage kadangare ke samun wuri.

Jarumi Adam A. Zango ya yi addu'a mai ratsa zuciya ga Rahama Sadau
Jarumi Adam A. Zango ya yi addu'a mai ratsa zuciya ga Rahama Sadau. Hoto daga adam_a_zango/instagram
Asali: Instagram

KU KARANTA: A dawo mana da mazakutarmu: Hotunan fusatattun matasa suna zanga-zanga a Benue

Jarumi Adam A. Zango ya yi wallafar a shafinsa na Instagram inda yace: "Innalillahi wa innna ilaihi raji'un. Allah ka nisanta ni da wadanda basa kishin masoyina.

"Ka nisantani da wacce ta janyo batanci ga ma'aikin Allah, Rahama Sadau. Allah ka shiryeta idan ta yi tuba ta gaskiya. Allah ka yaye mata girman kai.

"Allah yasa ta rinka karbar gyara cikin gaggawa. Allah ka daurata bisa hanya madaidaiciya. Idan kuma ba mai shiryuwa bace, Allah ka la'anceta.

"Shi kuma wanda yayi batanci ga shugabanmu, Allah ka nuna mana karshensa tun a duniya dama can tsinanne ne, Zindiki kuma mushiriki. Allah ya shiryamu, ka kara mana son Muhammadu Rasulullah".

KU KARANTA: Obaseki ya roki jami'an 'yan sanda da su koma bakin ayyukansu

A wani labari na daban, jarumar Kannywood, Rahma Sadau, ta fito fili ta yi magana a kan caccakar da aka yi ta yi wa hotunan da ta wallafa a kafar sada zumuntar zamani.

Idan ba'a manta ba, hotunan jarumar sun yi ta yawo a kafafen sada zumunta, bayan ta wallafa su, har mutane suka yi ta cewa sun saba wa addini da al'adarta.

Jarumar ta kara wata wallafa a kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, inda tace tayi dana sanin wallafa hotunan da suka janyo tsokaci na sabon Allah da manzonsa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel