Ni mai kare martabar addini da Annabi ne a duk inda nake - Rahama Sadau ta yi martani a kan wani tsokaci

Ni mai kare martabar addini da Annabi ne a duk inda nake - Rahama Sadau ta yi martani a kan wani tsokaci

- Nayi da na sanin wallafa hotuna na a kafafen sada zumunta, sakamakon tsokacin da ya taba addinina da Annabina, cewar Rahama Sadau

- Bayan jarumar Kannywood din ta wallafa hotunanta a kafafen sada zumunta, ta sha caccaka da raddi daga mutane daban-daban

- Ganin tsokacin da mabiyanta suka yi ta yi ne yasa ta kara wata wallafa, inda ta dakatar da duk wani mai zagin addininta da annabi Muhammad (SAW)

Jarumar Kannywood, Rahma Sadau, ta fito fili ta yi magana a kan caccakar da aka yi ta yi wa hotunan da ta wallafa a kafar sada zumuntar zamani.

Idan ba'a manta ba, hotunan jarumar sun yi ta yawo a kafafen sada zumunta, bayan ta wallafa su, har mutane suka yi ta cewa sun saba wa addini da al'adarta.

Jarumar ta kara wata wallafa a kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, inda tace tayi dana sanin wallafa hotunan da suka janyo tsokaci na sabon Allah da manzonsa.

Ta tsame kanta daga wadannan munanan kalamai, Daily Nigerian ta wallafa.

KU KARANTA: Da duminsa: Sabbin mutum 170 sun harbu da korona a Najeriya

Ni mai kare martabar addini da Annabi ne a duk inda nake - Rahama Sadau ta yi martani a kan hotunanta
Ni mai kare martabar addini da Annabi ne a duk inda nake - Rahama Sadau ta yi martani a kan hotunanta. Hoto daga @Dailynigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dakarun soji sun kashe 'yan ta'adda, sun bankado harin tawagar 'yan gudun hijira

Kamar yadda ta wallafa: "Salam, a gaskiya ban ji dadin ganin sakonni da cece-kuce a kan hotunan da na wallafa da a ganina basu da wata illa. A matsayina na 'yar adam, na yi dariya a kan wasu tsokacin wasu kuma sun sani takaici da alhini. Wadanda suka fi tayar min da hankali sune yadda wasu suka sauya salon al'amarin gabadaya.

"Ina da mabiya masu addinai daban-daban wadanda wasu suka yi tsokaci na sabon Allah, sai dai in ce subhanallah. Wasu kuma suna zagin fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW) - Wannan shine kololuwar sabon Allah, wanda ya ja nayi dana sanin wallafar tawa gabadaya.

"Duk wanda ya san ni ya san cewa bana tanka wa kowa koda zagina yayi, Amma a kan Annabina da addinina dole ne in dakatar da ko wanene.

"Ba zan lamunci zagi ko kuma cin zarafin addinina ba, ko wanene kuma a ko ina ne.

"Duk wadanda suka yi wannan su kiyaye, kuma yakamata su san darajar addinai. Ni mai kare martabar addini na da manzo na ce a duk inda na tsinci kaina."

A wani labari na daban, dangin fursunoni 1,181 daga cin wadanda suka gudu daga gidajen gyaran hali na Oko da Benin sun maido dasu da kansu, jaridar Leadership ta wallafa hakan.

Wata majiya daga gidan gyaran halin ta tabbatar da cewa 'yan uwan mutane 24 daga cikin wadanda suka gudu sun dawo dasu tare da lauyoyinsu a ranar 30 ga watan Oktoba, 2020, a bisa umarnin gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel