'Yan adawa ke daukar nauyin 'yan daba domin lalata mulkina - Gwamnan PDP ya koka
- Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya zargi 'yan adawa da daukar nauyin bata-gari wurin kawo cikas a ayyukansa
- Yayi wannan furucin ne yayin da yaje yawon duba ayyukansa na gyare-gyaren tituna cikin birnin Yola a ranar karshen mako
- A cewarsa, yakamata a yaba wa jajircewarsa wurin kashe dukiya don yi wa jiharsa ayyuka yadda ya dace, ba wai a dinga kawo cikas ba
Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri ya zargi wasu 'yan adawa da daukar nauyin 'yan ta'adda da bata-gari wurin kawo cikas a mulkinsa.
Fintiri yayi wannan zargin ne cikin ranakun karshen mako yayin da yake duba wasu ayyukansa a Yola, babban birnin jihar, Daily Nigerrian ta wallafa.
A cewarsa: "Bai dace ana daukar nauyin bata-gari ba don lalata kayan gwamnati, kamata yayi su zo su ga yadda muke amfani da dukiyar gwamnati wurin yi wa jama'a ayyuka."
Gwamnan ya ce, adawa mara ma'ana bata taimakon al'umma, ya nuna yadda yake amfani da dukiya wurin yi wa jiharsa aiki, don haka ya cancanki a yaba masa.
KU KARANTA: Dalilin da yasa ba za mu bayyana suna sojin da suka yi kisan Lekki ba - Rundunar soji
KU KARANTA: Binciken gida-gida: Shehu Sani ya yi martani mai zafi ga gwamnati
Ayyukan da ake kan yi a jihar, wadanda gwamnan yaje da kansa dubawa sun hada da titin Dougire, titin bayan gidan gwamnati, gidajen likitoci, layin Legas gaba da titin barikin sojoji, layin Falu da sauran wurare da ke cikin kananun hukumonin Yola ta arewa da ta kudu.
Bayan Fintiri ya sanar da hakan ya nuna niyyarsa ta gyara jiharsa, kuma ya lashi takobin komai rintsi sai ya karasa ayyukansa.
A cewarsa, "Nayi tunanin 'yan adawa za su zo su duba yadda muke tattalin dukiyar gwamnati wurin gyaran jiha. Duk da yadda bata-gari suka lalata dukiyoyin gwamnati, suka kuma balle ma'adanai a ranar Lahadi da Litinin, wanda hakan ya kawo cikas daga ayyukan."
A wani labari na daban, Haruna Ungogo, jakadan Najeriya a kasar Jordan, masarautar Hashmite da ke Jordan da Iraq, inda ya rasu yana da shekaru 75 da haihuwa.
Daily Nigerain sun tattaro bayanai a kan mutuwarsa a ranar Lahadi da safe a asibitin Garki da ke Abuja, bayan kwantar da shi da aka yi da kwana biyar.
Majiya daga iyalansa ta ce za a yi jana'izarsa a Kano ranar Litinin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng