EndSARS: Kada ku ji tsoro, ku fito mu tattauna - Buhari ga matasa

EndSARS: Kada ku ji tsoro, ku fito mu tattauna - Buhari ga matasa

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya roki matasa da su ajiye makamansu a ranar Lahadi, 1 ga watan Nuwamba

- Ranar ta kasance ranar matasa ta Afirika, wacce yayi amfani da wannan damar don isar da sakonsa ga matasa

- Ya ce tayar da hankula ba nasu bane, kamata yayi su zo su tattauna da gwamnati wurin kawo gyara a harkar tsaro

A jiya da daddare ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki matasa a Abuja, da su daina zanga-zanga a tituna, su yi kokarin tattaunawa mai amfani da gwamnati, wacce aka shirya musamman don gyara a kan dakatar da zalincin da 'yan sanda ke yi wa 'yan Najeriya.

Shugaba Buhari ya nuna rashin amincewarsa da amfani da karfi da matasa ke yi wurin tayar da tarzoma ga 'yan Najeriya da ba su ji ba ba su kuma gani ba, Vanguard ta wallafa.

KU KARANTA: Dalilin da yasa ba za mu bayyana suna sojin da suka yi kisan Lekki ba - Rundunar soji

EndSARS: Kada ku ji tsoro, ku fito mu tattauna - Buhari ga matasa
EndSARS: Kada ku ji tsoro, ku fito mu tattauna - Buhari ga matasa. Hoto daga @Vanguard
Asali: UGC

KU KARANTA: Matar aure nake bukata mai addini, da yanayi kadan na Nicki Minaj - Matashi

Yayi wannan rokon ne a wata takarda da ya fitar don murnar zagayowar ranar matasa wacce ake yi duk ranar 1 ga watan Nuwamba, wacce tayi daidai da ranar matasan Afirika.

Idan ba'a manta ba, matasa sun yi zanga zanga a kan rundunar SARS a makonnin da suka gabata, wanda hakan yayi sanadiyyar rushe rundunar.

Shugaban kasar da ya samu wakilcin ministan Abuja, Muhammad Bello, ya ce ya ji duk abubuwan da matasa ke rokonsa da ya aiwatar, kuma ya ce kada su ji tsoron fitowa fili don tattaunawa da gwamnati don kawo canji a kan 'yan sanda.

A wani labari na daban, hukumar sojojin Najeriya ta ce rundunar OSS, da aka samar don kawar da ta'addanci da garkuwa da mutane a arewa maso yamma, ta samu nasarar kashe 'yan ta'adda 5.

Sai dai sun rasa soja daya sakamakon bata - kashin da suka yi da 'yan ta'addan a kauyen Diskiru da ke karamar hukumar Faskari a jihar Katsina.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng