Dalilin da yasa ba za mu bayyana suna sojin da suka yi kisan Lekki ba - Rundunar soji

Dalilin da yasa ba za mu bayyana suna sojin da suka yi kisan Lekki ba - Rundunar soji

- Rundunar sojin Najeriya ta ce ba za ta gabatar da sunayen wani soja da yayi aiki a Lekki Toll gate ba a ranar 20 ga watan Oktoba

- Bayan kashe-kashen da ake zargin sojoji sun yi, mutane daga ciki da wajen Najeriya sun zargi gwamnati da sojojin da tazarta hakkin bil'adama

- Duk da sojoji sun musanta faruwar lamarin, kuma har yanzu babu wata hujja da ta tabbatar da hakan, face gawar mutum daya tak

Rundunar sojin kasa ta ce ba za ta gabatar da sunayen jami'anta da aka tura Lekki Toll Gate ba, a ranar 20 ga watan Oktoban 2020, The Cable.

Faruwar al'amarin ya janyo hankalin mutanen ciki da wajen Najeriya, yayin da aka zargi sojoji da gwamnatin tarayya da tozarta hakkin bil'adama.

Duk da rahotanni na nuna an kashe mutane da dama, amma har yanzu kisan mutum daya kacal aka tabbatar.

A wata tattaunawa da aka yi da Osoba Olaniyi, kakakin rundunar sojojin 81, sojojin da suka yi aiki a ranar basu amsa sunansu ba.

"Hakan ya ci karo da yadda jami'an tsaro ke gudanar da ayyukansu. A yadda mutane suka yi ta bayar da labarai, kamar muna yakar gwamnati ne, wanda hakan kuskure ne," a yadda jaridar ta wallafa.

Dama rundunar sojojin ta musanta faruwar lamarin.

A wata wallafa da rundunar sojoji suka yi a shafinsu na Twitter, sun ce labarin bude wutar da aka ce sojoji sun yi a toll gate karya ne.

Amma a makon da ya gabata, Olaniyi ya tabbatar da cewa sojoji suka yi wannan aikin.

Ya ce gwamnatin jihar Legas ce ta nemi sojoji da su tabbatar da samar da zaman lafiya bayan rikicin da ya barke.

"Ba tare da wata-wata ba sojojin Najeriya suka bude wa fararen hula wuta. Daga faruwar zanga-zangar EndSARS, babu wani soja da ke karkashin rundunoni 81 da ke jihar Legas da yayi wannan aika-aika," kamar yadda ya shaida a takardar.

KU KARANTA: Ku daina ba mu lambar yabo, kalubalantarmu za ku dinga yi - Wike ga 'yan jaridu

Dalilin da yasa ba za mu bayyana suna sojin da suka yi kisan Lekki ba - Rundunar soji
Dalilin da yasa ba za mu bayyana suna sojin da suka yi kisan Lekki ba - Rundunar soji. Hoto daga @TheCable
Asali: Twitter

KU KARANTA: Wurin wawushe tallafin korona, dattaijuwa ta rasa ranta a Kaduna

A wani labari na daban, hawaye sun kubce wa Goddy Jeddy Agba, karamin ministan wutar lantarki, a ranar Talata, 27 ga watan OKtoba, yayin da yake zagayen duba asarorin da matasa suka tafka wa Calabar, babban birnin jihar Cross River.

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, Agba ya fashe da kuka, bayan ganin irin aika-aikar da bata-gari suka yi a asibitin masu tabin hankali, inda suka lalata tsadaddun abubuwa.

Gwamna Ayade, ya bayyana irin dumbin dukiyar da jihar Cross River ke bukata don gyara duk abubuwan da aka bata. Read more:

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel