Matar aure nake bukata mai addini, da yanayi kadan na Nicki Minaj - Matashi
- Wani dan Najeriya ya bazama wurin kokarin nemo budurwar da yake so ya aura
- Saurayin, mai suna Ejike Analike, ya bayyana irin yanayi da surar matar da yake bukata
- Ya ce yana son mace mai addini, amma mai salo da diri irin na Nicki Minaj
Kowa da irin mata ko kuma miji da yake son ya karasa rayuwarsa da shi ko ita. Bayan kafafen sada zumunta sun bayyana, samun mata da mazajen aure ya saukaka ga mutane da dama.
Wani saurayi, mai suna Ejike Minimum Wage Analike, yayi amfani da shafinsa na kafar sada zumuntar zamani don neman matar aure.
Kamar yadda ya bayyana a wata matattara da ke kafar sada zumuntar zamani ta Facebook, inda yayi cigiyar matar da yakeso.
Ya wallafa hotonsa, sannan ya bayyana irin matar da yake so, hakan kuwa ya kawo cece-kuce iri-iri.
Kamar yadda ya wallafa, "Ina son budurwa wacce soyayyarmu za ta kai ga aure, amma wajibi ne ta zama mai saukin hali, mai alkibla, tsayinta daidai amma fa tazama mai yawan ibada kuma mai salo da diri irin na Nicki Minaj, 'yar asalin jihar Anambra."
Wannan wallafar tasa ta janyo cece-kuce iri iri, wanda wasu suke tabbatar masa da cewa ba zai taba samunta ba.
Wani Freddie lion cewa yayi: "Kawai ka halicceta da kanka."
Wani dianclif ya ce: "Ka fara bayyana mata da kudaden da ke asusunka na banki ta gani tukunna."
Wani Chuzzyofficial ya ce, "Gaskiya mafi yawanmu maza za mu so mace mai halayyar Mary amma ta zama mai salo irin na Cardi B. Matsalar dai ba mu san yadda hakan zai hadu waje guda a kan mace daya bane." Da sauran tsokaci iri-iri da samari da 'yan mata suka yi ta yi.
KU KARANTA: Binciken gida-gida: Shehu Sani ya yi martani mai zafi ga gwamnati
KU KARANTA: Ku daina ba mu lambar yabo, kalubalantarmu za ku dinga yi - Wike ga 'yan jaridu
A wani labari na daban, wata mata ta rasa ranta a daren Litinin yayin damben kwasar kayan tallafin COVID-19 a ma'ajiyar karamar hukumar Kaura dake Kagoro, Daily Trust ta wallafa haka.
Daily Trust sun bayyana yadda mamaciyar, Esther Mba, wacce take da shekaru a kalla 45 ta rasa ranta sakamakon damben dibar kayan tallafin.
Kamar yadda bayanai suka zo, bata-garin sun fara kwasar kayan abincin ne da misalin karfe 7 na daren Litinin, duk da harbe-harben jami'an tsaro da na 'yan sa kai, amma abin ya ci tura.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng