Gwamnati ta dura kan ASUU game da amfani da UTAS wajen biyan albashi

Gwamnati ta dura kan ASUU game da amfani da UTAS wajen biyan albashi

- Gwamnati ta caccaki matakin da kungiyar ASUU da ke yajin-aiki ta dauka

- Malaman jami’ar sun ce sam ba za su yi rajista da IPPIS ba, sai dai UTAS

- Mai magana da yawun bakin Ma’aikatar ilmin kasa ya ce ba za ta sabu ba

Gwamnatin tarayya ta yi tir da sharudan da kungiyar ASUU ta malaman jami’a ta bada na janye dogon yajin-aikin da ake yi a Najeriya.

Malaman jami’a sun bukaci ayi amfani da manhajar UTAS da su ka kirkira wajen biyansu albashi a madadin IPPIS da gwamnati ta kawo.

Gwamnati ta nuna ba za ta karbi wannan sharadi da shugabannin kungiyar ASUU su ka gindaya ba.

KU KARANTA: ASUU: Gwamnati za ta ba Malamai alawus

Mai magana da yawun bakin ma’aikatar ilmin tarayya, Ben Goong, ya nuna wannan sharadi da malaman jami’an su ka kawo ba zai sabu ba.

Ben Goong ya ce kungiyar malaman ba ta isa ta fada wa gwamnatin tarayya hanyar da za a bi wajen biyan ta albashin kwadagon da su ke yi ba.

ASUU ta ce: “Mun yi niyyar mu koma bakin aiki a ranar 21 ga watan Oktoba baya mun cin ma yarjejeniya da bangaren gwamnatin tarayya.”

Shugaban ASUU na kasa, Farfesa Bidoun Ogunyemi ya bayyana haka a lokacin da aka tambaye shi game da lokacin da za a bude makarantu.

KU KARANTA: Gwamna Zulum da Bello Matawalle su shiga cikin rikicin ASUU

Gwamnati ta dura kan ASUU game da amfani da UTAS wajen biyan albashi
Gwamnati da ASUU a taro Hoto: TVC
Asali: Twitter

Su dai shugabannin ASUU sun hakikance a kan cewa manhajar UTAS ta cikin gida ce, har kuma su na ganin gwamnati ta na daf da na’am da ita.

A lokacin da ASUU ta ke ganin yajin-aikin ya kusa zuwa karshe, gwamnati ta nuna ba haka ba.

Dazu kun ji Gwamnan Kogi ya na cewa zanga-zangar #EndSARS da ake yi ba komai ba ne face siyasar 2023 ce, sannan ya ce an ci riba da COVID-19.

Gwamna Bello ya kuma ce rufe mutane a gida da yajin aikin ASUU ya taimakawa zanga-zangar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel