Tir da goyon bayan masu zagin Islama – Shehu Sani ga Emmanuel Macron

Tir da goyon bayan masu zagin Islama – Shehu Sani ga Emmanuel Macron

- Ana zargin Emmanuel Macron da mara baya a ci mutuncin musulunci

- Shehu Shehu Sani ya maida wa Shugaban kasar Faransa martani a jiya

- Sani ya yi tir da Macron kan goyon bayan masu neman bata musulunci

Kalaman da su ka fito daga bakin shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron su na cigaba da jawo ce-ce-ku-ce a kasashe har da Najeriya.

Ana zargin shugaba Emmanuel Macron da yi wa musulunci rashin adalci bayan da ya yi wa addinin kudin-goro, ya ce shi ke jawo ta’addanci.

Bayan haka ana zargin gwamnatin Macron da nuna goyon baya ga masu yi wa musulunci batanci.

KU KARANTA: Yadda ake zaben Shugabanni a Musulunci - Ahmad Gumi

Daga cikin wadanda su ka maida martani ga shugaban kasar Turan har da tsohon Sanatan Kaduna a Arewacin Najeriya, Kwamred Shehu Sani.

Sanata Sani ya ce dole ayi tir da masu ta’addanci da rigar musulunci a kasar Faransa, sai dai wannan bai hana shi yin tir da aikin Macron ba.

‘Dan siyasar ya ce babu abin da zai hana a fito a yi tir da abin da shugaban kasar Faransar ya yi na ba masu yi wa addinin musulunci goyon-baya.

“Ya kai @EmmanuelMacron, dole ayi tir da duk wani harin ta’addanci ko zagon-kasa da aka yi a kasar Faransa da sunan musulunci, tsantsar hauka ce da tsantsangwaron rashin imani.”

KU KARANTA: Gololo ya caccaki Gwamnan adawa a kan goyon-bayan EndSARS

Tir da goyon bayan masu zagin Islama – Shehu Sani ga Emmanuel Macron
Emmanuel Macron Hoto: https:www.economist.com
Asali: UGC

Ya ce: “Mara baya kai-tsaye ko a kaikaice da ka ke yi ga masu bata musulunci ko cin mutuncin Annabi Muhammad (tsira da aminci a gareSa), duk shi ma abin ayi Allah-wadai ne.”

Sani wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya majalisar dattawa tsakanin 2015 zuwa 2019, ya yi wannan magana ne a shafinsa na Twitter a ranar Litinin.

A ranar Litinin kun ji cewa Paul Pogba ya daina buga wa kasar Faransa kwallo saboda Shugaban kasar Emmanuel Macron ya taba addinin Musulunci.

Ana rade-radin Pogba ya ki daukar cin kashin Gwamnatin kasar, ya yi ritaya daga buga wa gida.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel