Jami'an gwamnati sun yi min tallar kayan tallafin korona bayan sun boyesu - Buba Galadima

Jami'an gwamnati sun yi min tallar kayan tallafin korona bayan sun boyesu - Buba Galadima

- Ana zargin cewa kayan tallafin da fusatattun batagari ke kwashewa an yi niyyar karkatar dasu ne

- Gwamnatin tarayya da wasu kungiyoyi na 'yan kasuwa da masu zaman kansu sun bawa gwamnatocin jihohi tallafin kayayyaki domin rabawa talakawa

- Sai dai, a mafi yawan jihohi, tallafin ya gaza zuwa hannun talakawa har ya zuwa wannan lokaci da aka janye dokar kulle da takaita zirga-zirga.

Jigo a jam'iyyar APC, Buba Galadima, ya ce jami'an gwamnatin wata jiha da bai bayyana ba sun taba tunkarar ofishinsa domin sayar da kayayyakin tallafin korona da suka karbo daga gwamnatin tarayya.

Dattijon dan siyasar ya caccaki gwamnatocin jihohi a kan boye kayan abincin da 'yan kasuwa da kungiyoyi (CACOVID) suka bayar a matsayin gudunmawarsu domin tallafawa talakawa lokacin annobar korona.

Galadima ya bayyana hakan yayin da ya bayyana a wani shirin gidan talabijin din AIT da aka watsa kai tsaye ranar Litinin, kamar yadda jaridar The PUNCH ta rawaito.

KARANTA: An kashe jami'in kwastam a jihar Jigawa, an gudu da bindigarsa

"Na san jihar da jami'an gwamnatinta suka boye kayan tallafin korona a manyan shaguna tare da zuwa ofishina domin neman masu siyan irin wadannan kayan.

"Har sharadi suka gindaya cewa dole mai siyan kayan ya kasance ya fito daga wata jihar daban," a cewar Galadima.

Jami'an gwamnati sun yi min tallar kayan tallafin korona bayan sun boyesu - Buba Galadima
Buba Galadima
Asali: UGC

Da aka tambayeshi ko ya sanar da jami'an tsaro wannan bayani mai muhimmanci, sai Galadima ya mayar da matani da cewa, "ai ko yanzu haka suna sauraron abinda nake fada. Kar jami'an tsaro su kalli jawabina a matsayin na makiyi, ni dan kasa ne mai kishi da ya sadaukar da rayuwarsa domin fadin gaskiya".

KARANTA: Abuja-Kaduna: Masu garkuwa sun kashe Kanal a rundunar soji bayan karbar kudin fansa N10m

Galadima ya kara da cewa ya san abinda ya fada zai iya zama sanadin rasa rayuwarsa.

Gwamnoni suna cigaba da shan suka a kan zarginsu da boye kayan tallafin korona da suka karba daga gwamnatin tarayya da wasu kungiyoyi masu zaman kansu.

Sai dai, kungiyar gwamnoni (NGF), a ranar Litinin, ta musanta zargin cewa gwamnoni sun boye kayan abincin da aka basu domin rabawa talakawa a jihohinsu sakamakon dokar kullen da aka saka bayan bullar annobar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel