Zanga-zanga: Ministocin Buhari 2 sun mika kokon bararsu a gaban Sarkin Kano

Zanga-zanga: Ministocin Buhari 2 sun mika kokon bararsu a gaban Sarkin Kano

- Ministocin tsaro da gona sun kai ziyara fadar sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero

- Nanono da Magashi wadanda suka kasance yan asalin jihar sun roki Sarki Bayero da ya sanya baki don kawo karshen zanga-zanga a jihar

- Hakan na zuwa ne bayan Buhari ya umurci dukkanin ministocinsa da su koma jihohinsu don wanzar da zaman lafiya

Rahotanni sun kawo cewa, an yi kira ga sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero a kan ya sanya baki domin kawo karshen zanga-zangar da matasa ke yi a jihar.

Ministan tsaro, Bashir Magashi da takwaransa na noma, Sabo Nanono, wadanda suka kasance yan asalin jihar ne suka yi wannan kira kamar yadda jaridar Aminiya ta ruwaito.

Sun yi kiran ne a yau Litinin, 26 ga watan Oktoba, yayinda suka kai ziyara fadar sarkin.

Zanga-zanga: Ministocin Buhari 2 sun mika kokon bararsu a gaban Sarkin Kano
Zanga-zanga: Ministocin Buhari 2 sun mika kokon bararsu a gaban Sarkin Kano Hoto: HAUSAALL
Asali: Twitter

Sun bayyana cewa, sun kai ziyarar ne bisa umurnin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya bukaci kowani minista ya koma jiharsa domin samar da zaman lafiya.

A cewarsu ziyarar ta zo daidai da muradin gwamnatin jihar na wanzar da zaman lafiya a fadin jihar.

Da ya ke jawabi, Bashir Magashi ya ce ya wajabta a kansa a matsayinsa na jami’in samar da tsaro, ya tabbatar da an samu zaman lafiya a yankinsa.

KU KARANTA KUMA: An kuma: Bata gari sun ɓalle daƙin ajiyar abinci a Abuja, sun kwashe komai

Ministocin sun kuma bayyana irin tasirin da masu rike da sarautun gargajiya ke da shi wajen wanzar da zaman lafiya, tare da bukatar matasa da su zauna lafiya domin amfana da irin shirye-shiryen bunkasa rayuwar matasa da gwamnati ke bijirowa da su.

A nasa jawabin, sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya godewa shugaba Muhammadu Buhari bisa turo ministocinsa jihar don ganawa da jama’a a kokarin da gwamnati ta ke yi na tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Sarkin ya bayyana matasa a matsayin kashin bayan ci gaban kowace al’umma, ya kuma nemi hadin kan su wajen samar da zaman lafiya a jihar da ma kasa baki daya.

KU KARANTA KUMA: Bata gari sun kai farmaki cibiyar killace masu korona a Jalingo, sun yashe komai harda gadaje

A karshe, ya ba su tabbacin samun cikakken goyan bayan masarautar wacce ya ce kofarta za ta kasance a bude a kowanne lokaci wajen samar da zaman lafiya da ci gaban kasa.

A wani labarin, Buhari ya roki iyaye da su koro yaransu da duk wasu kayan alatu da suka koma da shi gida, wanda sun san ba za su iya siya da kansu ba, The Cable ta wallafa.

Ya sanar da hakan ne bayan zanga-zangar EndSARS ta tsawon sati guda, wacce ta ja bata-gari suka yi ta wadaka da dukiyar gwamnati da ta al'umma a fadin kasa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel