An kashe mutum 1 yayinda bata gari suka yi yunkurin kona ofishin yan sanda a Ibadan

An kashe mutum 1 yayinda bata gari suka yi yunkurin kona ofishin yan sanda a Ibadan

- Wasu bata gari sun kai mamaya ofishin yan sanda a yankin Mokola da ke Ibadan

- Sun yi yunkurin kona ofishin yan sandan amma matasa da ke yankin sun yi nasarar hana su

- Lamarin ya fara ne bayan harbin bindiga da ba a san daga ina ya fito ba ya halaka wani matashi

Wasu yan daba a safiyar ranar Lahadi, sun kai farmaki ofishin yan sandan Mokola da ke Ibadan, babbar birnin jihar Oyo, a kokarinsu na son kona ofishin.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa sai da matasan yankin suka shiga lamarin kafin aka iya hana yan daban kona ofishin yan sandan.

Daya daga cikin matasan da ke makwabtaka wadanda suka hana yunkurin kona ofishin, Musa Muhammed, ya bayyana cewa saura kadan a kashe wata inspekta mace.

An kashe mutum 1 yayinda bata gari suka yi yunkurin kona ofishin yan sanda a Ibadan
An kashe mutum 1 yayinda bata gari suka yi yunkurin kona ofishin yan sanda a Ibadan Hoto: Businessamalive
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buratai ya shiga labule da manyan kwamandojin rundunar soji kan zanga-zangar EndSARS

Ya kara da cewa a matsayinsa na shugaban matasa shine ya tara mutane suka dakile harin yan daban na kona ofishin yan sandan.

Ya kuma bayyana cewa rikicin ya fara ne dokacin da harbin bindiga ya kashe wani yaro da bai ji ba bai gani ba.

Ya ce babu wanda ya san daga inda harbin ya fito, amma matasan suka dauki gawar yaron zuwa ofishin yan sanda a Mokola, inda suke tunanin jami’in dan sanda ne ya harbe shi.

Musa ya ce a lokacin da yan daban suka isa ofishin yan sandan, jami’ai da dama da ke bakin aiki sun tsere inda suka bar inifam dinsu.

KU KARANTA KUMA: An kuma: Bata gari sun ɓalle daƙin ajiyar abinci a Abuja, sun kwashe komai

Biyo bayan lamarin, jami’an hadin gwiwa mai suna ‘Operation burst’ sun fito don dakile harin.

Wani babban jami’in Operation burst a jihar, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da lamarin amma ya karyata batun mutuwar matashin kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Sai dai, ya ce an kama yan daba bakwai, inda ya kara da cewa abubuwa sun daidaita a Mokola da kewayenta.

A gefe guda, mazauna jihar Kogi da ke Arewacin Najeriya sun fasa ma'adanar kayan tallafin COVID-19 da aka bai wa jihar.

Kamar kowacce jihar, sun kwashi iyakar kayan da za su iya kwasa sannan suka yi awon gaba da su, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Balle wuraren adana tallafin korona a jihohi ya fara daga yankin kudancin kasar nan bayan zanga-zangar EndSARS.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng