Allah ya yiwa AbdulMalik, dan marigayi Sheikh Jafar Mahmoud Adam rasuwa

Allah ya yiwa AbdulMalik, dan marigayi Sheikh Jafar Mahmoud Adam rasuwa

- Dan babban Malamin addinin Musuluci ya rasu ahadarin mota ranar Asabar

- Manyan malamai a fadin Najeriya sun aika sakon ta'azziyarsu ga iyalansa

Inna lil Laahi wa inna ilaiHi Rajiun! Allah ya yiwa AbdulMalik, 'dan gidan marigayi Sheikh Ja'afar Mahmud Adam rasuwa ranar Asabar, 10 ga watan Oktoba, 2020.

Legit Hausa ta samu labarin daga wajen ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr Isa Ibrahim ali Pantami, Sheikh Abdullahi Umar Gadon Kaya da Sheik Dr Mansur Sokoto ta shafukansu na Facebook.

A cewar Minista Pantami, " Na samu labarin rasuwar AbdulMalik, 'dan Shaykh Ja'afar Mahmud Adam (RH).

Ina mika ta'aziyya zuwa ga yan'uwansa da iyayensa, kan Allah Ya jikansa, Ya jikan iyayenmu da sauran yan'uwanmu, kuma Ya kyautata namu bayan na su,...

"Wanda ya mutu, bai yi sauri ba. Mu da muke nan bamu dade ba, sai mun zo"... in sha Allah"

A cewar Dr Mansur Sokoto, matashi AbdulMalik ya rasu ne sakamakon hadarin mota.

"Yanzu muke smaun labarin mun rasa danmu Abdulmalik Jafar Mahmud Adam cikin wani hatsarin mota, " cewar Dr Sokoto.

Allah ya yiwa AbdulMalik, dan marigayi Sheikh Jafar Mahmoud Adam rasuwa
Credit: Dr Mansur Sokoto
Asali: UGC

DUBA NAN: Bidiyon yadda aka soka wa wani wuka a rumfar zabe a Ondo

A wani labarin mai tashe, Wani jami'in hukumar yaki da masu ta'amulli da miyagun kwayoyi na kasa (NDLEA) Samuel Birma ya rasa ransa sakamakon duka da aka masa a Adamawa bayan da masu safarar kwayoyi suka masa sharrin ya yi garkuwa da su.

An ruwaito cewa Birma da abokan aikinsa sun kamo wasu da ake zargin masu safarar miyagun kwayoyi ne a Michika za su kai su Yola yayinda matasan suka kai musu hari.

KU KARANTA: Yan sanda sun damke tsohuwar da ta sayar da jikanta N1.3m saboda uban bai biya sadaki ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel