An kuma: Bata gari sun ɓalle daƙin ajiyar abinci a Abuja, sun kwashe komai

An kuma: Bata gari sun ɓalle daƙin ajiyar abinci a Abuja, sun kwashe komai

- Wasu bata gari sun kai farmaki sashin masana’antu da ke yankin Idu, Abuja inda suka balle dakin ajiyar kayayyaki

- Haka zalika bata garin sun far ma rumbun ajiya na hukumar NEMA, sannan suka yashe kayan abinci da aka ajiye a ciki

- Lamarin ya afku ne a ranar Lahadi, 25 ga watan Oktoba, yayinda matasa ke ta barna a sassa daban-daban na kasar

Bata gari a ranar Lahadi, 25 ga watan Oktoba, sun yashe wani rumbun ajiya mallakar hukumar bayar da agajin gaggawa ta tarayya (NEMA) a yankin Jabi adali Biu.

Har ila yau, bata garin sun kai farmaki ga rumbun ajiya na masana’antu masu zaman kansu a yankin Idu, babbar birnin tarayya, sun sace kayayyakin abinci.

KU KARANTA KUMA: Garin daɗi na nesa: Gwamna Zulum ya rabawa zawarawa N65m a garin Rann

An kuma: Bata gari sun ɓalle daƙin ajiyar abinci a Abuja, sun kwashe komai
An kuma: Bata gari sun ɓalle daƙin ajiyar abinci a Abuja, sun kwashe komai Hoto: Wothappen
Asali: UGC

A yayin mamayar, yan iskan sun sace buhuhuna da dama na kayan abinci, shinkafa, kwalayen madara, galolin man gyada, abincin gwangwabi, kwalayen taliya, da dai sauransu.

Yan bata garin sun sha karfin jami’an yan sanda a wajen, jaridar ThisDay ta ruwaito.

Mafi akasarin barayin sun zo ne da adaidaita sahun da babura domin cika su da kayan da suka sata.

Yankin Idu na dauke da masana’antu masu yawan gaske wadanda ke dauke da rumbun ajiya domin adana kayayyaki.

KU KARANTA KUMA: Jerin manyan ma'aikatu da ɓata garin Filato suka lalata, ciki har da sakatariyar jihar

A gefe guda, gwamnonin jihohi 36 na Najeriya sun karyata boye kayan abincin tallafin COVID-19 da kungiyoyi masu zaman kansu suka samar don sassautawa talakawa radadin zaman gida lokacin kullen COVID-19.

Kungiyar manyan 'yan kasuwa da kamfanoni wadanda suka taru suka kira kansu da CACOVID, sun hada biliyoyin nairori don taimakon 'yan Najeriya a kan cutar Coronavirus, wacce tayi ajalin mutane a kalla 1,139, sannan ta shafi mutane 62,992.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel