Femi Gbajabiamila ya ce dole a biya diyyar wadanda #EndSARS ta rutsa da su
- Femi Gbajabiamila ya ziyarci jihar Legas yau bayan zanga-zangar #EndSARS
- Shugaban majalisa ya sha alwashin karbowa wadanda su ka yi asara hakkinsu
- Gbajabiamila ya ce gwamnatin Legas ta na neman N1tr a dalilin asarar da ta yi
Shugaban majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila ya ce dole ayi adalci ga iyalan duk wadanda aka kashe wajen zanga-zangar EndSARS.
Rt. Hon. Femi Gbajabiamila ya jajanta wa wadanda su ka rasa na-kusa da su a dalilin kashe-kashen da aka yi, ya ce dole kasar nan ta zauna lafiya.
KU KARANTA: Fafaroma ya roki al’ummar Duniya su sa Najeriya a addu’a
Gbajabiamila ya yi tir da kashen masu zanga-zanga, ya ce hakan bai kamata ya maimaita kansa ba.
“Na zo daga Abuja yau ba domin kurum in nuna ina tare da shi (Gwamna) ba, har da mutanen jihar Legas. Wadannan kwanaki ne masu nauyi.” Inji sa.
Ya ce: “Bayan na taho daga filin jirgi, in zauna a nan tare da gwamnan ina kallon abin da ya faru na abubuwan da su ka faru, ya na sa mu bakin ciki.”
“Na tabbata su kansu masu zanga-zangar sun yi nadamar yadda abin ya yi nisa, ya kai ga haka.”
KU KARANTA: #EndSARS: APC ta yabawa kokarin shugaba Buhari
Shugaban majalisar ya cigaba da jawabi, “daga yadda na fahimta, wadanda su ke goyon bayan #EndSARS, da masu adawa duk sun fada matsala.”
Gbajabiamila ya ce majalisa za ta yi kokarin ganin an yi adalci a kan abin da ya faru, ya kuma nemi a daina yi wa lamarin kallo da madubin kabilanci.
"Yanzu nan Gwamnan Legas ya fada mani sake tada Legas zai ci kusan Naira tiriliyan 1. Da na tambayi gwamna, ya ce mani ya na kasafin kusan N1tr."
A ranar Lahadi aka ji cewa Bola Tinubu ya bayyana cewa shi ne ainihin wanda ya mallaki kamfanonin yada labaran nan na The Nation da TVC.
Tinubu ya ce ya san za ayi wa kamfanonin na sa barna wajen zanga-zanga, amma ya yi gum.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng