Kona TVC da The Nation: Gudun a zubar da jini ya sa Bola Tinubu ya yi hakuri
- Bola Tinubu ya ce ya na da labarin za a kai wa The Nation da TVC hari
- ‘Dan siyasar ya bayyana cewa duk da haka bai sa sojoji su taba kowa ba
- Tsohon Gwamnan Legas ya ce bai da burin ganin an zubar da jinin wani
Asiwaju Bola Tinubu ya bayyana haka ne a jawabin da ya fitar a ranar Lahadi, 25 ga watan Oktoba.
Babban jigon na jam’iyyar APC mai mulki ya yi wa wannan jawabi na sa taken: “The #EndSARS protests; a fundamental lesson in democratic governance”.
KU KARANTA: Bai dace a harbi masu zanga-zanga ba - Obasanjo
An samu wasu bata-gari da su ka rika kona shaguna da gine-ginen Bayin Allah da na gwamnati bayan an zargi jami’an tsaro da harbe masu zanga-zanga.
Daga cikin wuraren da aka kai wa hari har da gidan talabijin na TVC da kuma kamfanin jaridar The Nation, wadanda ake zargi Tinubu duk ya mallake su.
Bola Tinubu ya tabbatar da cewa akwai kudinsa a wadannan kamfanonin biyu, amma ya nesanta kansa da hannu wajen kula da kofofin shiga kasuwar Lekki.
“A gefe guda, babu shakka ni ne mai kamfanin jaridar The Nation da tashar TVC.” Inji Tinubu.
KU KARANTA: An kona ofishin 'Yan Sanda wajen zanga-zanga

Asali: UGC
“An kai mana hari, an barnata kayan aiki sosai, Ko da cewa mun samu bayani kafin a kawo harin, ban kira kowa ina neman bukatar sojoji ko ‘yan sanda ba.”
‘Dan siyasar ya ce bai sa jami’an tsaro su tsare dukiyoyin na sa ba, har kuma a kai ga cewa ya sa an raunata ko kashe wasu. Ya ce: “Ba na so a zub da jini.”
Kwanaki wasu sun fito su na zargin Bola Tinubu da hannu a zanga-zangar #EndSARS, Tsohon Gwamnan ya ce sharri kurum wasu miyagu sus ke yi masa.
Asiwaju Bola Tinubu ya ce an yi masa wannan mugun sharri har a cikin fadar Shugaban kasa.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng