Jerin manyan ma'aikatu da ɓata garin Filato suka lalata, ciki har da sakatariyar jihar

Jerin manyan ma'aikatu da ɓata garin Filato suka lalata, ciki har da sakatariyar jihar

- Ana ci gaba da samun tashe-tashen hankula sakamakon zanga-zangar EndSARS a wasu sassan kasar

- Bata gari na ci gaba da sace-sace a hukumomin gwamnati da shagunan mutane masu zaman kansu

- A Filato, bata gari sun kai farmaki manyan ma’aikatu da dama harda sakatariyar gwamnatin jihar

Wasu bata gari sun kai farmaki sakatariyar jihar Filato, kamfanin buge-buge na Filato (PPC), kamfanin jaridar Najerian Standard Newspaper, da ma’aikatar ruwa ta jihar, duk a garin Jos.

Mista Tanimola Obasa, jami’in hulda da jama’a na hukumar NSCDC, ya tabbatar da lamarin a ranar Lahadi, 25 ga watan Oktoba, a garin Jos.

A cewar Obasa, bata garin, wadanda suka aiwatar da mummunan aiki wanda baya bisa doka a ranar Asabar, sun kuma fasa dakin ajiyar kaya na hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) da na hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar (SEMA).

Har ila yau ya ce sun sace kayan abinci da sauran kayayyaki, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Jerin manyan ma'aikatu da ɓata garin Filato suka lalata, ciki har da sakatariyar jihar
Jerin manyan ma'aikatu da ɓata garin Filato suka lalata, ciki har da sakatariyar jihar Hoto: @vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Jihar Filato: Ɓata gari sun ɓalle ɗakin ajiyar taki da kayan aikin gona, sun kwashe komai

Ya ce barayin, wadanda suka fasa ginin a kokarinsu na neman kayan tallafin korona, sun lalata dukiya sannan suka sace wasu muhimman abubuwa.

“A jiya, wasu yan bata gari sun fasa dakin ajiyar kaya na NEMA da SEMA sannan suka sace kayan abinci da sauran kayayyaki.

“Sai da muka tabbatar da cewar basu taba dukiyoyin mutane masu zaman kansu ba, amma abun ya fi karfinmu.

“Sun kuma lalata sakatariyar jihar, hukumar ruwa da sauran gine-ginen gwamnati sannan suka sace wasu muhimman abubuwa.

“Mun yi iya bakin kokarinmu domin hana bata garin aiwatar da mummunan aikin, amma saboda bama so abun ya zama rikici, munyi taka tsan-tsan wajen amfani da karfi,” in ji shi.

Mista Paul Jatau, wani babban edita a kamfanin jaridar Nigerian Standard Newspaper, ya bayyana cewa bata garin sun lalata ginin da ababen hawa mallakar ma’aikatan kamfanin.

KU KARANTA KUMA: Wata sabuwa: Miyetti Allah ta bankaɗo wanda ke ɗaukar nauyin Zanga-zanga

Sai dai Mista Jatau, wanda ya kasance Shugaban kungiyar yan jaridar Najeriya (NUJ) reshen Filato, ya ce babu wanda ya rasa ransa ko ya ji rauni a harin.

Ya ce doki da hukumomin tsaro suka kai cikin lokaci ya daidaita lamarin.

Har ila yau, Mista Nangor Ndam, jami’ in hulda da jama’ a na ma’aikatar ruwa, ya tabbatar da cewar yan iskan sun tafi da muhimman abubuwa daga hukumar.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel