Dennis Amachree ya ce Hadiman Sanata ne su ka dauko ‘Yan daba a Abuja

Dennis Amachree ya ce Hadiman Sanata ne su ka dauko ‘Yan daba a Abuja

- Kwanaki an ga wasu cikin bakaken kaya su na daukar ‘Yan daba a mota

- Wani tsohon jami’in tsaro da ya ga bidiyon, ya ce ba jami’an DSS ba ne

- Dennis Amachree ya ce Hadiman wani Sanata ne su ka yi hayar tsageru

Wani tsohon mataimakin darektan DSS, Dennis Amachree ya yi magana game da wani bidiyo da ya rika yawo, inda aka ga ana daukar ‘yan daba a mota.

Dennis Amachree ya ce mutanen da aka gani cikin bakaken riguna tamkar jami’an hukumar DSS ba ma’aikatan tsaro ba ne, ya ce hadimin wani Sanata ne.

Amachree ya bayyana haka ne dai a lokacin da ‘yan jarida su ka yi hira da shi jiya a gidan talabijin na Channels Television a wani shiri da ake yi da hantsi.

KU KARANTA: Batutuwa da jawabin Shugaban kasa a kan #EndSARS su ka kunsa

Tsohon ma’aikacin ya ce yadda jami’an DSS su ka yi kokari har su ka bankado wadanda aka gani a wannan bidiyo, ya kamata sojojin kasa ma su yi hakan.

Sojoji sun musanya zargin su na da hannu a harbe-harben da aka yi a Lekki, Legas, su ka ce wasu ne su ka yi shigarsu, ba tare da sun bayyana su wanene ba.

“Na yi waya a hedikwata na bincika. Wadannan mutane ma’aikatan wani Sanata ne. Idan kuwa haka ne, idan tunanin su kama su kawai.” Inji Amachree.

KU KARANTA: Ya kamata ayi amfani da dattaku kan dambarwar #EndSARS – JNI

Dennis Amachree ya ce Hadiman Sanata ne su ka dauko ‘Yan daba a Abuja
Shugaban Najeriya Hoto: Channelstv
Asali: UGC

A lokacin da aka fara ganin wannan bidiyo na wasu masu kama da jami’an tsaro su na daukar tsageru a cikin mota, an yi zargin DSS ne da wannan aiki.

Da ‘yan jarida su ka tuntubi mai magana da yawun bakin DSS, Peter Afunaya, ya musanya zargin, ya ce ba su iya gane wadanda su ka yi wannan mugun aiki ba.

Dazu kun samu labari cewa Gwamnan Benuwai ya gamu da martanin jagoran APC saboda ya nuna goyon baya ga masu zanga-zangar#EndSARS a Najeriya.

Garus Gololo ya nemi Matasa su rabu da #EndSARS, su yi wa Samuel Ortom zanga-zanga.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel