Shugaban kasa zai yi wani abu a kan zanga-zangar da ake yi inji Monguno

Shugaban kasa zai yi wani abu a kan zanga-zangar da ake yi inji Monguno

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da Shugabannin Hafsun Sojoji

- NSA ya ce nan gaba kadan za a ga matakin da gwamnatin tarayya za ta dauka

- Babagana Monguno ya yi kira ga matasa su guji bata sunan Najeriya a Duniya

Babagana Monguno ya ce shugaba Muhammadu Buhari zai dauki mataki a game da zanga-zangar #EndSARS da ya barke a bangarorin Najeriya.

Mai ba shugaban kasar Najeriya a kan harkar tsaro ya bayyana wannan bayan zaman majalisar tsaro da aka yi a yau Alhamis, 22 ga watan Oktoba, 2020.

Janar Babagana Monguno mai ritaya ya shaida wa ‘yan jarida wannan bayan sun shafe sa’a uku su na kus-kus da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

KU KARANTA: Mayakan Boko Haram rututu sun mika wuya - MNJTF

Babagana Monguno ya ke fadawa ‘yan jarida a fadar shugaban kasa cewa: “Duk mun san cewa mu na cikin wani irin hali mai kamari da ya damu kowa.”

Hadimin shugaban kasar ya ce lamarin da ake ciki ya fi damun mai girma Muhammadu Buhari.

“Shugaban kasa (Buhari) ya umarci gwamnati ta yi duk abin da ya kamata domin ganin an cin ma matsaya a kan wannan rikici” inji Janar Monguno mai ritaya.

Ya ce: “Zuwa yanzu gwamnati ta amince da bukatun masu zanga-zangar. Bayan nan kuma da alamu masu zanga-zangar sun kama wata hanya da ba a so.”

KU KARANTA: Tinubu ya soki harbe ‘yan zanga-zanga da aka yi cikin duhun dare

Monguno ya ce: “Shugaban kasa ba ya son abin ya kai yadda tsaro zai tabarbare, komai ya cabe.”

“Yanzu shugaban kasar ya bar ofis, zai shawo kan lamarin. Ina sa ran nan da sa’o’i kadan zai yi abin da zai shawo kan matsalar, duk kasa ta cin ma matsaya.”

Janar din ya ce shugaban kasa ya gargadi jami’an tsaro da yin abin da zai kawo matsala, tare da kiran matsa su guji bata sunan Najeriya a gaban Duniya.

Jiya bayan rikicin Lekki ya lafa, Gwamna Jide Sanwo-Olu ya fadi yadda ya yi da fadar Shugaban kasa lokacin da ake harbin masu zanga-zangar #EndSARS.

Gwamnan na Legas ya ce ya kira Shugaban kasa Buhari a waya sau 2 amma aka ce ba ya ofis.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng