Da ɗuminsa: Buhari na jagorantar zaman majalisar tsaro ta ƙasa yanzu
- Shugaba Muhammadu Buhari na shugabantar zaman majalisar tsaro ta kasa
- Taron ya samu halartan mataimakin shugaban kasa, manyan shugabannin tsaro da kuma wasu ministoci
- Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ta tsinci kanta a wani yanayi na fargaba da tashin hankali
Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jagorantar taron majalisar tsaro ta kasa a fadar Shugaban kasa da ke Abuja, a yau Alhamis, 22 ga watan Oktoba.
Taron wanda ke gudana a kowani zangon shekara, na zuwa ne a yayinda ake tsaka da fuskantar tashe-tashen hankula a sassa daban-daban na kasar.
Wadanda suka halarci taron sun hada da mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo, sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa, Ibrahim Gambari da kuma mai ba kasa shawara a harkar tsaro, Janar Babagana Monguno.
KU KARANTA KUMA: Shugaban ƙasa 2023: Jerin sunayen mutane 5 da PDP ta fitar, ɗaya zai gaji Buhari

Asali: Twitter
Sauran sune Shugabannin tsaro karkashin jagorancin Shugaban ma’aikatan tsaro, Janar Gabriel Olonisakin; Shugaban hafsan soji, Laftanal Janar Tukur Buratai.
Sai Shugaban sojin ruwa, Vice Admiral Ibok Ekwe Ibas da Shugaban rundunar sojin sama, Air Marshal Sadique Abubakar.
Har ila yau, Sufeto Janar na yan sanda, Mohammed Adamu, Darakta Janar na hukumar DSS, Yusuf Bichi, Darakta Janar na hukumar liken asiri, Ahmed Rufa’i duk sun hallara.
KU KARANTA KUMA: Zanga-zangar EndSARS: Obaseki ya ba fursunonin da suka tsere nan da Juma'a su koma
Ministocin da ke wajen sune; Bashir Magashi (tsaro); Rauf Aregbesola (harkokin cikin gida), Mohammad Dingyadi (harkokin yan sanda) da kuma Geoffrey Onyeama(harkokin waje).
Hadiman shugaban kasa, Bashir Ahmad da Buhari Sallau sun tabbatar da zaman a wani wallafa da suka yi a shafinsu na Twitter.
Ana sa ran taron zai mayar da hankali a kan rikicin da ake fama da shi a yankunan kasar, musamman a jihar Lagas.
A wani labarin, Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya ce ya nemi kiran shugaba Muhammadu Buhari domin ya fada masa ana harbe masu zanga-zanga.
Mista Babajide Sanwo-Olu ya bayyana cewa bai yi nasarar samun shugaban kasar a wayar salula ba, domin kuwa da ya kira, an fada masa ba ya nan.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng