Tinubu: An samu wadanda su ka je su ka fada wa Buhari ni na haddasa zanga-zanga
- Asiwaju Bola Tinubu ya ce babu abin da ya hada shi da #EndSARS
- Tsohon Gwamnan ya ce har an yi masa sharri a fadar Shugaban kasa
- Tinubu ya yi tir da yin amfani da harsashi a kan masu zanga-zanga
Bola Ahmed Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas, ya karyata rade-radin ke yawo, ya ce sam bai da hannu a zanga-zangar #EndSARS da ake yi.
Jagoran jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi hira a gidan talabijin na Channels TV, inda ya karyata zargin da ake yi masa.
A cewar Bola Ahmed Tinubu, wasu mutane sun je gaban shugaba Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa, inda su ka kai masa munafuncinsa.
KU KARANTA: Gwamnan Legas ya garzaya asibitoci, ya ga wadanda aka harba a Lekki
Da ya ke magana bayan ya wanke kansa, Bola Tinubu ya yi tir da harbe masu zanga-zanga da wasu mutane da ak zargin sojoji ne su ka yi a jihar Legas.
Ana zargin sojoji sun buda wa ‘yan zanga-zanga wuta a Lekki, wannan ya faru ne a ranar Talata.
Da aka yi magana da Tinubu ta wayar salula a wani shiri a gidan talabijin, ya kuma ce babu sisin kobonsa a cikin kamfanin Lekki Concession Company.
“Ba zan taba goyon bayan duk wata barna ba. Ba za ayi da ni ba. Me zai sa su yi amfani da dalma?”
KU KARANTA: Sai Gwamnati ta tashi tsaye ko abubuwa su rincabe mata - Obasanjo

Asali: Facebook
Ya ce: “Kafin yanzu an zarge ni, har aka fada wa fadar shugaban kasa cewa ni na shirya zanga-zangar, wai ni na ke daukar nauyin zanga-zangar.”
A dalilin wannan zanga-zanga da ya barke, an kona kamfanin gidan jaridar The Nation da gidan talabijin na TVC da ake zargin Tinubu ya mallaka.
A ranar Larabar aka yi hira da Dahiru Bauchi arediyo, shehin ya ja-kunne cewa ba a kashe wuta da wuta, don haka ya nemi a sasanta da masu zanga-zanga.
Babban malamin ya ce idan aka yi sake karshen zangar-zangar #EndSARS ba zai yi kyau ba.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng