Kisan wadanda su ka fita zanga-zangar #EndSARS ya girgiza kungiyar EU

Kisan wadanda su ka fita zanga-zangar #EndSARS ya girgiza kungiyar EU

- Kungiyar Turai ta yi magana game da harbe wadanda su ka fita zanga-zanga

- EU ta nuna cewa ta na goyon bayan masu zanga-zangar EndSARS a Najeriya

- Josep Borrell ya fitar da jawabi na musamman a madadin EU a ranar Laraba

Kungiyar kasashen Turai ta EU ta tofa albarkacin bakinta game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya, inda matasa ke ta faman zanga-zanga.

EU ta ce harbe Bayin Allah masu zanga-zanagar #EndSARS ya girgiza ta. Kungiyar ta fitar da jawabi ne a jiya ranar 21 ga watan Oktoba, 2020.

Jaridar Punch ta rahoto kungiyar ta kasashen Turai ta na cewa ta na goyon bayan kiran da wasu ke yi na gyara sha’anin aikin ‘yan sanda a fadin kasar.

KU KARANTA: Gwamna Sanwo-Olu ya yi magana a kan kisan masu zanga-zanga

EU ta fitar da jawabi ne ta bakin mataimakin shugabanta, Josep Borrell a ranar Laraba da yamma.

Mista Josep Borrell wanda ya na cikin manyan wakilan EU ya soki yadda jami’ai su ka hallaka mutane saboda kurum sun fita zanga-zangar lumuna.

Borell mai shekaru 73 a Duniya, shi ne ke rike da kujerar Ministan harkokin waje na kungiyar EU, bayan nan kuma ya na lura da sha'anin tsaro na Turai.

“Abin tada hankali ne a fahimci mutane da-dama sun mutu, wasu sun samu rauni wajen zanga-zangar da ake yi domin nuna adawa ga dakarun SARS.”

KU KARANTA: Dahiru Bauchi ya ba Gwamnati da masu zanga-zanga shawarar ayi sulhu

Kisan wadanda su ka fita zanga-zangar #EndSARS ya girgiza kungiyar EU
Masu zanga-zangar #EndSARS Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Josep Borrell ya cigaba da jawabi da cewa: “Ya na da matukar muhimmanci a hukunta wadanda su ke cin zarafin jama’a bayan an same su da laifi.”

“Bayan alwashin da gwamnati ta yi na kawo sauye-sauye, mu na sauraron ganin an yi aiki.”

A jiya kun ji cewa Olusegun Obasanjo ya yi wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kashedi game da kashe masu zanga-zanga da ake yi a wurare.

Olusegun Obasanjo ya ce kashe ‘yan zanga-zangar zai jawo wa Gwamnati karin matsala.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel