Hillary Clinton tayi kira ga Buhari, Soji, su daina kashe masu fafutukar #EndSARS
- Hilary Clinton ta soki kisan da aka yi wa masu zanga-zangar #EndSARS
- Tsohuwar ‘Yar takarar Amurkan ta yi kira ga gwamnati ta dauki mataki
- Ita ma Tauraruwar nan, Rihanna ta yi tir da abin da ke faruwa a Najeriya
Tsohuwar ‘yar takarar shugaban kasar Amurka, Misis Hilary Clinton ta tsoma baki game da abin da ke faruwa a wasu jihohin Najeriya.
A ranar Talata, Clinton ta bukaci dakarun sojoji su daina hallaka matasan da su ka fito su na kira a gyara sha’anin aikin ‘yan sanda a Najeriya.
KU KARANTA: Amurka ta rufe ofishinta a Najeriya saboda rikicin #EndSARS
A jiyan ne ake zargin jami’an sojoji sun buda wuta ga masu zanga-zanga a Lekki, hakan na zuwa ne bayan gwamnatin Legas ta sa dokar ta-baci.
Misis Clinton mai shekaru 72 a Duniya ta na cikin wadanda su ka fito su ka fara sukar wannan mummunan abu da ya faru a jihar Legas.
Daga lokacin da Clinton ta yi wannan magana da karfe 11:00 na dare (agogon Najeriya) zuwa yanzu, kusan mutane 200, 000 su ka yada sakon.
Wannan gajeren jawabi na Clinton ya samu karbuwa a shafin Twitter, inda sama da mutane 180, 000 su ka nuna sun yi sha’awar maganar.
KU KARANTA: Legas ta yi asarar sama da N200m a dalilin zanga-zangar #EndSARS
“Ina kira ga Muhammadu Buhari da sojojin kasan Najeriya, su daina kasashe matasa masu zanga-zangar #EndSARS.” Inji Clinton.
Tsohuwar sakatariyar gwamnatin ta kara da kira da babban murya ta ce #StopNigeriaGovernment.
Haka zalika Mawakiya Rihanna ta ce ba za ta iya kallon zaluncin da ake yi wa 'yan zanga-zangar ba.
A jiya ne shugaban Majalisa ya ce ba zai amince da kundin kasafin kudin 2021 sai an amince da kudin biyan diyyar wadanda SARS su ka kashe.
Majalisa ta bada sharudan amincewa wannan kafin ta yi na'am da kasafin da aka gabatar.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng